Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Matasa 16 Da Ake Zargi Da Jagorantar Fadan Daba A Kwaryar Birnin Kano.

Spread the love

 

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta samu nasarar cafke matasa 16 wadanda ake zargi da dawo harkar fadan Daba, a unguwannin Sharada, Ja’en da kuma Dala.

Kakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya Aikewa manema labarai.

Sanarwar ta ce, a ranar 18 ga watan Yuni 2024, rundunar ta samu rahotan fitowar gungun yan Daba, a unguwar Ja’en Makera, wadanda suka farwa wani kwamandan bijilanti mai suna Muktar Garba, har sai da suka illatashi, tare da wasu mutane 2.

Jami’an yan sandan sun Yi gaggawar Kai wadanda lamarin ya ritsa da su, zuwa Babban asibitin Kwararru na Murtala Muhammed, inda likita ya tabbatar da rasuwar Muktar Garba.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya Kara da cewa an Kama mutane biyu , da suka hada da Umar Shuaibu mai shekaru 25 dake unguwar Ja’en Makera da kuma Umar Kabiru mai shekaru 19 Wanda akafi sani da ( Nakamore Mamore) wadanda ake zargi da jagorantar Aiyukan daban, da ya Kai ga hallaka jami’in bijilantin.

Haka zalika Rundunar ta Kama wasu Matasa uku, da suka hada da Adamu Ado ‘Ramos’ Mazaunin Dan Dinshe, Ibrahim Ahmad ‘Abban Layya’ Mazaunin Dala da kuma Abubakar Abdullahi ‘Tulu’ , wadanda Rundunar ta ke nema ruwa a jallo sakamakon zargin aikata laifukan Daba.

Tunda fari Rundunar ta samu rahotan mutuwar wani matashi mai suna Bukari Tijjani, a yankin Dala, Wanda ya rasu a wajen Fadan Daba.

Wannan nasarar ta samu sakamakon samun bayanan sirrin da rundunar Yan Sandan ta Yi daga Ranar 15 zuwa 20 ga watan Yuni 2024, inda aka cafke 11 daga cikin wadanda ake zargi da aikata Daba , inda aka samu muggan makamai da kwayoyi.

A karshe Rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *