Rundunar yan sandan jahar Kano ta gurfanar da wani matashi mai suna Zaharaddin Yusuf, a gaban lotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Kurna ,bisa zarginsa da shiga ta laifi ba da izini ba, cin mutunci da kuma gwada kwarfi.
Bayan gurfanar da shi ne mai gabatar da kara, Isah Danzuru, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa , inda nan ta ke ya amsa laifin gwada karfin ya yin da ya musanta sauran laifukan.
Tunda fari ana zarginsa da zuwa gidan mai kara, ya dinga dukanta bayan ya ji labarin cewa ta ce bashi da aikin yi kamar yadda idongari.ng ta ruwaito.
Alkalin kotun mai shari’a Shamsuddin Ado Abdullahi, ya sanya shi a hannun beli, saboda bata hakuri da ya yi, kuma kotun ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Yuni 2024, don ma su gabatar da kara su gabatar da shaidu.
- EFCC Ta Soma Binciken Kwankwaso Kan Badaƙalar Naira Biliyan 2.5
- Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 624 cikin watan Mayu