Rundunar ‘yan sandan Abuja ta kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su

Spread the love

A wani samame da rundunar yaki da garkuwa da jama’a ta ‘yan sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja da ke garin Rubochi na karamar hukumar Kuje ta aiwatar a kauyen Ukya da ke kan iyaka da jihar Nassarawa ta samu nasarar tseratar da wadanda masu garkuwa suka sace su 14.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta fitar, rundunar ta ce sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan kaddamar wa wurin da masu satar jama’a suke, inda kuma masu garkuwar da jama’a suka fara da bude wa ‘yan sanda wuta.

Kaunar Murja Kunya ya ratsa cikin zuciya ta don haka ku Aura mun ita: Ustaz Assalafi

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

To sai dai ‘yan sandan sun ce hakan ne ya sa jami’ansu suka mayar da wutar abin da ya yi sanadiyyar kashe mai garkuwar guda daya sannan sauran suka ranta a na kare tare da raunukan harbi a jikinsu.

Ba mu ne muka yi sanadin kaɗe saurayi da mota a Jibiya ba – Kwastam

Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Mawaƙi Kan Hana BBC Amfani Da Kiɗansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *