Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.

Spread the love

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga a sansaninsu da ke unguwar Mpape, a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, ya ce an kai samamen ne a ranar 9 ga watan Fabrairu bayan samun bayanan sirri.

Ya ce, sun yi nasarar kashe wasu kasurguman mahara a maboyar.

Ya ce sun hallaka kasurgumin dan bindigar da ya addabi yankunan Mpape, Bwari a Abuja, Kagarko a Kaduna, Masaka da kuma kauyen Nukun a Jihar Nasarawa.

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Kaunar Murja Kunya ya ratsa cikin zuciya ta don haka ku Aura mun ita: Ustaz Assalafi

A cewarsa, maharan sun jima suna satar mutane tare da karbar kudin fansa.

Kazalika, ya ce sun samu nasarar kai farmakin ne a maboyarsu da ke wani tsauni a Mpape tare da kwato makamai.

Adejobi, ya ce sun kwato makamai da suka hada da wayoyin hannu, layin waya, laya da kuma kwayoyi.

Ragowar sun hada da alburusai, adda, wukake da sauran muggan makamai.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *