Rundunar yan sandan jahar Bauchi ta yi nasarar kama mutane 673 da ake zargi da laifukan, garkuwa, fashi, Damfara, sata,a shekarar 2023.

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Bauchi, CP Auwal Muhammad Musa, ya bayyana cewa sun samu nasarar kama mutane 673 , da ake zargi da aikata laifuka mabam-banta a shekarar 2023 tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jahar ya bayyana hakan ne, ga manema a shelkwatar rundunar a ranar Asabar .

Ya ce, sun fara duba tsarin tsaron jahar sakamakon makotar da suka yi da jahohin Jigawa, Kano, Gombe,Taraba, Yobe, Kaduna da kuma jahar Plato dan dakile aiyukan batagari.

Cikin wadanda aka cafke , sun hada da masu garkuwa da 85 , sai wadanda ake zargi da kisan kai su 118 , yan fashi da makami 106 , sai Ta’adda, Satar shanu da masu fyade 86, sai wadanda suka yi yunkarin kashe kansu su 23,
Ana kuma zargin mutane 26 da laifin sata, mutane 81 da ake zargi da mallakar dukiya ta hanyar cutar jama’a da kuma masu siyan kayan sata su 19.

Haka zalika rundunar ta kama mutane 11 da ake zargi da laifin cuta da kunna wuta, Dan damfara 1, masu tada hankalin al’umma 14, da kuma mallakar makami ba bisa ka’ida ba su 15.

Kwamishinan yan sandan jahar ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata ta 2023, an rasa dukiya da ta kai sama da naira miliyan sittin da biyu da dubu dari takwas da chasa’in 62,890,000.00, ya yin da suka samu nasarar kwato naira miliyan talatin da daya da dubu dari da goma 31,110,000.00.

Sauran kayan da rundunar ta kwato , sun hada da Ababen hawa guda 15, bindiga kirar AK47 guda 16, bindigar harbin tsintsaye 20, shanu 70, Tumaki 60 da kuma harsasan bindiga AK47 guda 317.

Haka zalika rundunar ta samu nasarar hallaka masu garkuwa da mutane 20, a musayar wutar da suka yi da jami’an yan sandan jahar.
CP Auwal Musa ya godewa gwaman jahar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir , bisa hadin kan da yake ba wa rundunar a koda yaushe.

Ya kuma godewa babban sufeton yan sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu Egbetokun, da taimakaon da yake bayarwa dan tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Ya kuma yaba wa sauran hukumomin tsaro, kungiyoyin sa kai da al’ummar jahar da irin addu’o’in da suke yi da taimako wajen wanzar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *