Rundunar Yan Sandan Jahar Jigawa, Ta Yi Holen Mutanen Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Mabam-Banta

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Jigawa, ta yi holen wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka maban-banta dake jahar.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar DSP Shiisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya raba wa manema labarai da yammacin jiya Alhamis.

Çikin wadanda ake zargin, sun hada da, Yan Ta’adda, Yan fashi da makami, Ma su barnata dukiya, Kisan kai, Ma su fasa shagunan jama’a da kuma wadanda aka Kama da laifin Fyade.

DSP Shiisu Adamu , ya ce sun kuma  gabatar da wasu da ake zargi da hallaka tsohon Manajin Darektan Jigawa Housing Authority,  Alhaji Abubakar Babangida Muhammed, da abokansa biyu.

Rundunar ta yi nasarar kwato bindigu kirar AK47 guda 2, Harsasai 68, Babur,da kudi sama da naira dubu dari 200 da sauran miyagun kwayoyi.

Haka zalika an kwato wayar lantarkin da ake zargin an barnata.

Kakakin Yan sandan jahar Jigawan , ya Kara da cewa, an kama wasu Matasa biyu da ake zargin su, da balle shagunan al’umma suna yi mu su sata, inda aka sace kadarori na sama da naira miliyan 1.

A karshe ya ce dukkanin wadanda ake zargin za a gurfanar da su, a gaban kotu don su fuskanci hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *