Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke masu satar kananan yara su 9

Spread the love
Wadanda ake zargi sune a tsaye, yaran da aka ceto kuma sune a zaune

Rundunar  yan sandan jahar Kano, ta cafke wasu mutane 9 da ake zargi da satar kananan yara tare da siyar da su a kudancin Nijeriya.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake gana wa idongari.ng , a shelkwatar rundunar da ke Bompai Kano a ranar Alhamis.

CP Gumel ya ce, an dade ana safarar kananan yaran tare tafiya da su wasu gurare ,a fadin kasarnan, kuma rundunar ta samu nasarar ceto yara 7 daga hannun batagarin mutanen.

Tunda fari asirin wata mai suna Comfort Amos mai shekaru 45, ne ya tonu a tashar hawa motaci ta Mariri Kano, da ta ke yunkurin hawa mota domin tafiya da wani karamin yaro Abdulmutallib Sa’ad mai shekaru 5 , da aka sato daga jahar Lagos don kai shi jahar Lagos.

Ƴan sanda na neman waɗanda suka yi wa wani yaro mummunan kisan gilla a Zariya – Idongari.ng

A wajen ne aka gano cewar yaron baya jin turanci da harshen Igbo sai yaren Hausa kawai , inda aka fara yi wa matar tambayoyi har aka cafke ta, inda aka ci gaba da farautar sauran a jahohin Kano, Bauchi,Gombe, Lagos, Delta, Anambra Imo da dai sauran su.

Sauran wanda ake zargi da safarar yaran sun hada da , Chika Ezugbu mai shekaru 52 mazauniyar Sabon Gari Kano, Joy Nzelu mai shekaru 43 sabon Gari Kano, Clement Ali shekaru 35 mazaunin Badawa Kano, Emeka Ekedigwe mai shekaru 55 mazaunin Sabon Gari Kano.

Sauran sun hada da Ruth Yarima mai shekaru 45, mazauniyar Zango Bauchi, Aner Samuel mai shekru 35 mazaunin Yelwa Bauchi, Ebere Eriobuna mai shekaru 59, mazauniyar Anambra.

Yaran da aka ceto sun hada da, Abdulmutallib Sa’ad mai shekaru 5 , wanda aka sauya wa suna Ifenyi Chukwu da aka sace daga jahar Bauchi , aka siyar dashi kan kudi naira dubu dari hudu da tamanin 480,000, sai kuma Asiya Muktar mai shekaru 4 , da aka sauya wa suna zuwa Chioma , wadda aka sato daga jahar Bauchi, aka kuma siyar da ita kan kudi naira dubu dari hudu da tamanin 480,000 da kuma Muhammad Bilyamunu mai shekaru 3, da aka sauya wa suna Chioma, wanda aka sace daga jahar Bauchi aka kuma siyar dashi kan kudi naira dubu dari hudu da hamsin 450,000.

Sauran yaran sune Usman Adamu mai shekaru 8, da aka sauya wa suna zuwa Chibuke , kuma an sato shi daga Bauchi har aka siyar dashi naira dubu dari hudu da tamanin, Hafizu Hassan mai shekaru 8, daga jahar Bauchi wanda aka sauyawa suna zuwa Uche Chukwu , aka siyar dashi kan kudi naira dubu dari hudu da tamanin 480,000, sai kuma Chiamaka Ambrose mai shekaru 7 , wadda aka sace ta , a gadon asibitin Yelwa dake jahar Bauchi bayan an haifeta , aka siyar da ita kan kudi naira dubu 300,000 na karshen shi ne Muhammad iliyasu mai shekaru 5 da aka sato daga jahar Bauchi tun yana da shekara 3 , aka kuma sauya masa suna Chidebere , har aka siyar dashi naira dubu dari biyar a jahar Anambra.

Kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel ya ce da zarar sun kammala za su gurfanar da su agaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Tuni dai iyayen yara suka bayyana rin cikin su , ta dagoewa rundunar an sandan jahar Kano , bisa namijin kokarin da suka yi wajen dawo da yaransu.

Yanzu haka dai yarinya daya ce kawai ake neman iyayen ta,  wadda aka sace tun tana jaririya a asibitin Yelwa a jahar Bauchi, shekaru bakwai da suka gabata, amma sauran yaran duka sun hada da iyayensu.

Ko a shekarar 2019 sai da rundunar ta samu nasarar kama gungun barayin yaran su 7 tare da ceto yara 9, da ake yin sarafar su zuwa jahar Anambara kuma tuni wata babbar kotun jahar Kano ta yanke wa Poul One hukuncin daurin shekaru 104 a gidan yari sakamakon samunsa da kotun ta yi laifuka 38 da ake tuhumarsa da aikata wa na yin safarar yaran daga birnin Kano.

IDONGARI.NG

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *