Rundunar yan sandan jahar Kano, ta yi wata ganawa ta musamman tsakanin ta da ma su ruwa da tsaki, don warware ricikin manoma da Makiyaya, da ya shafe kusan shekaru 40, ana samun tashin sa a yankin karamar hukumar Makoda ta jahar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, (Bawahala) ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da Idongari.ng, a ranar Laraba.
Taron dai ya hadar da wakilan gwamnatin Kano, Sarakunan gargajiya, Malaman addinai, Hukumomin Tsaro, Masarautar Bichi, Hakimin Makoda da Kunchi, bangarorin da ke riciki da juna da kuma shugabancin riko na karamar hukumar Makoda , don samun fahimtar juna na warware ricikin .
SP Adullah Haruna Kiyawa, ya ce, an tattauna muhimman batutuwan da suke haifar da ricikin da kuma hanyoyin da za a bi wajen warware su.
DSS ta gargaɗi NLC kan ƙudurinta na shirya zanga-zanga
MNJTF ta halaka ƴan ta’adda a ƙasashen da ke fama da Boko Haram
Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, wato ( Fada da cika wa) wanda Mukaddashin Kwamishinan yan sandan DCP Umar Ahmed Chuso, ya wakilta , ya ba su tabbacin cewar , rundunar za ta ci gaba da yin aikin ta bisa Doka da oda, don Kare rayukan al’umma da dukiyoyin su.
Kwamishinan yan sandan ya buka ce su, da su ba wa, rundunar hadin kai da ba Su bayanan da za Su taimaka wajen dakile ricikin Manoma da Makiyaya.
Da ta ke jawabi maitaimaka wa gwamnan jahar Kano, Malama Mainuna UMar Shariff, ta ce gwamnatin Kano, za ta dauki matakin da yafi dace wa na Kawo karshen ricikin Manoma da Makiyaya.
Haka zalika shugaban karamar hukumar Makoda na rikon kwarya, Alhaji Mohammad Umar Gwale, ya ce za Su yi duk mai yiwuwa na lalubo bakin zaren waraware matsalar.
A karshe kwamishinan Yan sandan ya ja hankalin su da su guji daukar doka a hannun su, inda taron ya yi armashi wajen samun fahimtar juna sakamakon tattaunawar da aka yi.
IDONGARI.NG