Rundunar yan sandan jahar Jigawa, ta cafke wani matashi mai suna, Usman Ahmed dan shekaru 23 mazaunin unguwar Hotoro Kano, bisa zarginsa da hadin baki wajen samar da mummunan rauni da kuma fashi da makami.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Jigawa, DSP Shiisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce jami’ansu dake aiki a ofishin yan sanda na Gumel, ne suka kama wanda ake zargin ya na tuka wani babur kirar Daylong, mara Namba a yankin Gagarawa.
Sanarwar ta ka da cewa lokacin da jami’an yan sandan ke yi wa matashin tambayoyi ya gaza bayar da gamshasshiyar amsar da zata tabbatar da baburin mallakarsa ne.
Binciken yan sanda na farko-farko, ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shaida yan sandan cewa ya yaudari mai baburin zuwa hotel din Sahara dake Gumel , inda ya yi amfani da kwalaba ya bugawa masa akansa, sannan ya daba masa wuka a sassan jikinsa, har ya barshi cikin jini kafin ya gudu da baburin.
jaridar idongari, ta ruwaito cewa bayan an kama wanda ake zargin, jami’an yan sandan dake gudanar da sintiri sunga wani mutum cikin jini , inda suka garzaya da shi zuwa babban asibitin Gumel, don kula da lafiyarsa.
Sannan Rundunar ta kama Wani matashi, Mai suna Mustapha Ibrahim, bisa Zargin chanjawa matane katin cirar kudi ( ATM) tare da damfararsu, Inda aka kwato naira Dubu dari shida na wadanda ya chuta.
DSP SHISU, ya kara da cewa sun kuma kama Wani Mai suna , da Zargin satar motar sashin kiwon lafiya a matakin farko ta jahar Jigawa, a kokarin da yake Yi na Fita da ita daga jahar.
A karshe Rundunar ta ce dukkan wadanda ake Zargin sun amsa laifinsu, kuma da zarar an kammala bincike za a Gurfanar da su a gaban kotu.