Rundunar Yan Sandan Jigawa Ta Yi Holen Wadanda Ake Zargi Da Aikata Laifuka Maban-banta.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa , ta yi holen wadanda ake zargi da aikata laifukan Fashi da makami, Barnata dukiya, Barayi da dai sauransu , a shelkwatar rundunar dake Dutse.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar DSP Shiisu Lawan Adamu, ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai.

Cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da Bindiga kirar gida pistol guda 2, bindigar Harbin tsintsaye da kuma Harsasai tare da wasu Buhuna cuke da wayoyin al’umma da na gwamnati wadanda aka lalata.

” abun takaicin shi ne tun daga jahar Benue Suka taho jahar Jigawa , da Buhuna suna yanke lalata wayoyn ” DSP SHIISU LAWAN “.

Saurari Karin Haske daga Kakakin Yan sandan Jigawa DSP SHIISU Lawan Adamu

Haka zalika Rundunar Yan Sandan ta Kara yin kira ga al’umma da su ci gaba da bata bayanan sirri , Wanda zai Tamika Mata don dakile Aiyukan batagari, kuma a dinga Kare dukiyar gwamnati don ta al’umma ce baki daya.

DSP SHIISU Lawan, ya shawarci mazauna karkara da su Samar da yan Sakai don taimaka wa wajen sanar da Jami’an Tsaro wani Abu da ba su amince da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *