Rundunar Yan Sandan Kano Ta Bankado Wani Korarren Kwansitabul Da Ya Yi Mata Karya A Faifen Bidiyo.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta nemo wani korarren kwansitabul, da aka ganshi a wani faifen bidiyo a shafukan sada zumunta, inda ya yi zargin cewar korarsa aka yi bayan ya samu larula a gadon bayansa sakamakon wani aiki da aka tura su.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bidiyon da aka ga mutum mai suna, Aminu Abdullahi, ya fadi abubuwa da dama a cikinsa wadanda duka ba gaskiya ba ne, kuma hakan ne ya sanya kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya bayar da uumarnin nemo duk inda yake don rabe aya da tsakuwa.

A faifen bidiyon da ya karade shafukan sada zumuntar, anga mutumin yana ikirarin cewar ya yi aikin dan sanda , kuma an tura su wani aiki, don tabbatar da tsaro a wani waje da aka yi fashi da makami har ya samu ciwo a bayansa, daganan DPOn da yake aiki a karkashin ya korashi saboda bashi da lafiya.

Sai dai rundunar yan sandan Kano, ta ce abubuwan da ya fada a cikin bidiyon da mamaki , kuma bayaninsa yana dauke da matsaloli domin ba da shi akaje aikin da ya ce ya samu rauni a bayansa ba.

A cewar kakakin yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Aminu Abdullahi ya taba yin aiki a ofishin yan sandan Sheka, kafin daga bisani ya yi aiki a Mariri, an taba gurfanar da shi a gaban kotu saboda mari da ya yi, sannan kuma a ofishin yan sanda na Mariri dalilin da ya sanya aka kore shi, shi ne rashin zuwa wajen aiki, domin a lokacin da mahaifinsa yake da rai sai da ya zo ya bayar da hakuri.

Yan sandan sun nemi Tsohon dan sandan ya bayar da hakuri, amma yaki bayar wa, inda ya ce aikin ya isheshi kuma ya kawo takadda a rubuce bayan ya cire Kakinsa.

‘’ babu wanda ya kore shi , shi ya nuna cewar ya gaji da aiki da kansa yaga damar ajiye wa.

Suma wasu yan sanda da suka taba yin aiki tare, sun bayyana cewar, ikirarin da tsohon abokin aikin na su ya Yi,  ba gaskiya ba ne, domin babu shi akaje aikin da ya bayyana a faifen bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta.

Aminu Abdullahi , shi ne korarren kwansitabul din , ya ce abubuwan da ya bayyana a cikin faifen bidiyo , ya yi hakan ne don yaja hankalin jama’a, amma yana ba wa rundunar yan sandan hakuri bisa karyar da ya yi mata.

Tuni dai al’umma suka tafkara muhawara a shafin sada zumuntar Facebook kamar haka.

Anas MB

ko wanda yake brekete family da za’abi diddigin abun da kyau saika samu akwai sherri sosai cikin maganganunsu kasan shi talaka duk sadda aka samu matsala dashi da wani mai karfi ko hukuma to kawai shine da gaskiya alhali ni banga azzalumi ba duk kasar nan kamar talakawa kalli dai yadda masifar talaka ta jawo mana bala’i cikin kasar da hannunsu suka mikamu wurin mugun mutum

Ibrahim Hausawa Abu Mus’ab  ·

Ni dai Allah ya yafemin kuma Hukumar “yan sanda ta yafemin domin munsha zama dashi a wajen Malam Imrana mai Goro yana bamu wannan labarin, mu kuma muna tsinuwa da Allah wadai.

Shi kuma Allah ya shiryeshi. Sannan zanga da wace fuska zai dawo ya kalle mu.

Shamsiya Amin Madaki  ·

Allah sarki, Allah ya bada ikon a tallafamasa ameen, dan Allah Abdullahi Haruna Kiyawa

Kutaimakeshi Allah zetaimakeku Kuma

Wallahi yabani tausayi

Barma Al Munir  ·

Da jumawa mun dena yarda da labari daga bangare daya bisa umarnin Allah cewa a bincika, ko Malaman nan masu tafsirin idan ana kawo su nan gaskiya zasu yi ta bamu hakuri akan karya wa al’ummah. Allah baya son karya

Baffa Idiris Adam

nifa daman yanzu na daina yanke hukunci daga jin bayanin bangare daya har sai naji na daya bangaren.

Allah ya kyauta, shi kuma Allah ya kawo masa dauki

Ahmad Hudu Abdul

Ina jin yace DPO y kore Shi na CE shasha sha ne wlhi kuma wlhi yawancin masu irin wannan kaddarar a aikin gwanati wani bawan Allah suka xalunta ya CE Allah ya ISA shine masomin mtsalr su

Busiri Muhammad Soran Dinki  ·

Gaskiya mal haruna kana kokari

Allah yasa ka gama aikinka cikin aminci

Bello S Justice

Nifa tun da naji maganar shi nasan akwai rashin gaskia a ciki wlh, saboda babu yadda za ayi DPO ya karbe masa uniform kuma ya kore shi

Yusuf Abubakar Ameen

Dsp allah yakara maka lpy da nisan kwana

Aminu Mustapha Usman

Hmmm

Mutum kenan. Tin farko yasan yanason aikin meya kaishi ya kori kansa, shine sbd yanzu rayuwa ta juya masa baya kuma saiyayiwa wasu sharri sbd bashida adalci, har ya fadawa duniya yasa a dauka gaske ne.

Shiyasa duk abinda mutum zaiyi ya dinga tunanin gobensa. Alamunsa talauchi ne ya dameshi, da ya zamansa a aikinsa ko baiyi arziki ba, bazai tagaiyara irin haka ba.

Kunyi kokari sosai da kukayi bincike kuma kuka ƙaryatashi a idon duniya.

Allah yasa mudace

Kabiru Sule Inuwa

Kabiru Sule Inuwa

Haka nake son bincike daki daki dan gano gaskiya matsala.

Mal. Abdullahi Haruna Kiyawa.

Muhammad Alhaji Usman  ·

Agaskiya daa Ace duk yan sanda musanman ma PRO’s haka suke aikin su na kokarin warware abubuwa, Da Al-umma da dama ba zasu fahimci aikin Dan sanda ta Baibai ba. Ni a Yobe nake amah gaskiya kana kokkari sosai, and insha Allah duk sanda na shigo Kano zan kawo ma Ziyara har ofis. Allah ya kara Girma

ABDUL WAHAB  ·

Shikansa yanzu yayi danasanin barinsa aikin inakyautata zaton yayi videone Watakila mutanen gari suji tausayinsa sutaimaka masa dubada halinda kasarmu takeci anfi gaskata zalunci samada adalci Amma harga Allah baikyautaba Sam Sam yasa mutane sunyita tsinuwa abanza

Sulaiman Mohd Dorayi

Ranka ya dade Dan Allah ku taimaka masa domin da ganin Yana cikin damuwa matuka akwai depression atare dashi kuma bayan haka ana karbar kebur Sanfurin Tinubu Dan Allah aduba ataimaka masa.

Shamsu Ayuba

Gaskiya haruna kana kokari matuka Abinda kawai zamuce Allah yasa kagama wannam ae lfy Albarkacin Rahmansa

Habeeb Sani Jumare

Kai Kai gaskiya wannan mutumin wallahi Bai kyautaba

Kiyawa Allah ya sakamaka Da Alkhairi

Da hukumar yansanda Baki Daya

Sani Usama Bagari Funtua

Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa duniya da lahira ya kare ka da kariyansa daga dukkan sharrin,bala’i,musifa da asara Allah ya kara daukaka ya sa ka gama aikin nan lafiya.

Habibun Baba Hajjhabeeb

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!!!

KAI JAMA’AYANXU DAMA WANN BAWAN ALLAHN XAMA YAYI YATSARA ABINDA YA FADA A WANN CAN VIDEON

RAYUWA KENAN” ALLAH YASA MUGAMA LAFIYA”

GASKIYA DAMA DUK ME NUTSUWA IDAN YA SAURARI WAN CAN BAYANAN NASA XAI SAN AKWAI ALAMOMIN TAMBAYA ACIKI”

ALLAH YA KYAUTA” ALLAH YABASHI LFY”

YANXU MENE RI BARSA ANAN ?

KAFITO KACE A TEMAKA MAKA MANA KAI TSAYE”

AMMA KUMA KAWAI SAI MUTUM YAXU ƘALO ƘARYA

King Salim

Duk wanda yasan ya zagi ‘Yansanda’ yaje Bompai yanemi gafara

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *