Rundunar Yan Sandan Kano Ta Bayyana Sunayen Matasa 13 Da Ake Zargi Da Aiyukan Daba.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana sunayen wasu Matasa 13 da ake zargi da aikata laifukan Daba a sassan birnin jahar , inda ta bukace su da su kan su shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai .

Kakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da aike wa da manema labarai a Ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, an samu karuwar fadan Daba, a kananan hukumomi uku na kwaryar birnin Kano, wadanda Suka hada da Gwale, Dala da kuma Municipal.

Jerin sunayen matasan da ake zargin
hada da, Halipa Here, Sheye Injiniya, Yusuf Ilu, Walidi Auwalu Kapinta, Tijjani Rattagu, Agiri Balarabe, Dan Kasuwa da Dan Makare.

Sauran su ne , Nasiru Madada, Hali Pan Pan, Jamilu Piye, Saiyadu Zawai da kuma Inyasi.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bukaci Alumma da su ci gaba da ba wa rundunar hadin kan da ya dace, don kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *