Rundunar Yan sandan Kano Ta Bukaci Al’umma Su Nuna Kishin Kasa Da Zaman Lafiya Gabanin Hukuncin Babbar Kotun Tarayya

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da zaman lafiya da kishin kasa a daidai lokacin da babbar kotun tarayya ke shirin sauraren kararrakin da suka shafi rikicin masarautar Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

Kiyawa ya nanata kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da gargadi kan duk wani yunkuri na tada zaune tsaye.

Da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, rundunar ‘yan sandan za ta tabbatar da hana duk wata zanga-zangar jama’a, ko jerin gwano wanda dama tuni gwamnatin jihar kano ta haramta .

“Masu zanga-zangar da masu daukar nauyinsu za su fuskanci hukuncin shari’a. Za a tura isassun jami’an tsaro don tabbatar da doka da oda.

“An yi kira ga jama’a da su ba jami’an tsaro hadin kai tare da samar da bayanan da suka dace don kiyaye zaman lafiya da gano masu son ta da husuma a jihar.

“Ana shawaetar ‘yan banga da mafarauta, da su guji shiga duk wasu ayyukan tsaro ta kowacce fuska a jihar,” in ji shi.

KADAURA24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *