Rundunar yan sandan Kano ta cafke barayin wayoyin salula tare da kwato 39.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar kama wasu matasa biyu da ake zargi da satar wayoyin salula guda 39.

Mai mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce wadanda ake zargin sun sato wayoyin salular ne daga Nyanya Mararraba a jahar Nasarawa don su kawo Kano su siyar.

Tun a ranar 17 ga watan Didamban 2023, dakarun yan sandan suka samu bayanan sirrin kan batagarin matasan su biyu, da suka hada da Abbah Aminu mai shekaru 23, mazaunin Lungun Sharifai Kofar Mata Kano da kuma Zulkifilu Bello mai shekaru 30 mazaunin Pantami tashar Mota a jahar Gombe.

An samu wayoyi kira daban-daban har guda 39, inda rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike zata gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *