Rundunar Yan Sandan Kano Ta Cafke Mutane 105 Da Zargin Aikata Laifuka A Watan Satumba

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka su 105 cikinsu harda masu safarar miyagun kwayoyi da yan fashi da makami da kuma masu satar ababen hawa.

Kwamishainan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai Kano.

Bakori ya ce wannan nasara ta samu ne bisa umarnin babban sufeton yan sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu Egbeokun, kan amfani da dabarun zamani nah ana aikata laifuka , da kuma aiki kafada-kafada tare da al’umma musamman a wadannan watanni na karshen shekara , wanda akan samu yawan zirga-zirgar mutane da ababen hawa da yawaitar kasuwanci da kuma lokacin girbin amfanin gona.

A cewarsa rundunar yan sandan Kano, ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaro , musamman ta hanyar ‘’Operation Kukan  Kura’’, wanda ya taka rawar gani wajen dakile dukkan nau’o’in laifuka da tabbatar da da tsaro ga al’ummar jihar.

Abokin aikin Mujahid Wada ya ruwaito mana ’Operation Kukan  Kura, wani shiri ne na musamman da aka tsara don magance dukkan nau’o’in laifuka a Kano, tare da hadin kan al’umma, wanda aikin ya samar da gagarumar nasarar dakile aikata ta’addanci da kuma barazanar tsaro tun kafin su faru, ta hanyar yin amfani da al’umma da basira da kuma fasahar zamani.

Wadanda ake zargin sun hada da yan fashi da makami 17, masu safarar miyagun kwayoyi su 8, barayin motoci 9 da masu satar Adaidata sahu 5 da yan Daba 57da sauran masu sace-sace 9.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigu kirar AK-47 guda 3, bindigu kirar Pistol guda 3, bindigu kirar Revolver guda 3, bindiga kirar gida AK4-7 guda 1, Bindiga Doguwa kirar gida 1 da bindigu gajeru kirar gida guda 2.

Sauran sune albusai 7 da kwanson harsasai guda 5 wadanda aka yi amfani da su.

Haka zalika an kwato baburan adaidata sahu na sata guda 2, Babura 13 da shanu guda 3 da kuma motoci guda 7.

Kwamishinan ya kara da cewa an kwato takubba 38,Adduna 42, Wukake 58 da sauran karafa 31.

CP ya ce dakarunsu karkashin jagorancin baturen yan sandan Rijiyar Zaki, SP Jamilu Bala sun yi nasarar kama Fatiki 603 na kwayar Tramadol wadanda darajarsu ta kai naira miliyan sittin da dubu dari uku ( 60,300,000) da kuma kwalaye 6 na kwayar Pregabalin wanda kudinsu ya kai naira miliyan ashirin da biyu da dubu dari hudu da ashirin da biyar ( 22, 425,000).

Haka zalika baturen yan sandan Rijiyar Zaki, SP Jamilu Bala, sun sake kama sinkin tabar wiwi guda 523 bayan samun sahihan bayanan sirri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *