Rundunar Yan Sandan Kano Ta Cafke Mutane 26 Tare Da Kwato Wayoyi 126 Cikin Kwanaki 12.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta sake samun gagarumar nasarar kama kama wasu mutane 26 tare da kwato wayoyin sata guda 126,  a kokarin ta na murkushe ragowar burbushin sauran Yan Daba da ma su kwacen wayoyin al’umma  da kuma yan fashi da makami a fadin jahar.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ne ya bayar da umarnin fadada sintiri don kakkabe ragowar bata garin da suke addabar al’umma har aka cafke mutane 26.

Cikin kayayyakin da rundunar ta kwato sun hada da wayoyin salula 126,  Exol 600, Diazepam 20, sinki-sinkin tabar Wiwi 3, Wukake, Adduna 2, Almakashi 2, Na’ura mai kwakwalwa 2 da dai sauransu

Wannan nasarar na zuwa ne a sumamen da rundunar yan sandan jahar ta fara daga ranar 1 ga watan satumba zuwa 12 ga watan satumba 2024 don kakkabe burbushin ma su kwacen waya da yan fashi da makami a kwaryar birnin Kano.

SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa yanzu haka batun yana babban sashin gudanar da binciken laifuka na CID, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *