Rundunar yansandan jihar Kano ta ce za ta aiwatar da dokar gwamnatin jihar da ta haramta duk wani nau’in taro da zimmar gudanar zanga-zanga a faɗin jihar.
Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano CP Muhammad Ussaini Gumel, ne ya bayyana hakan ta Wata sanarwa da kakakin rundunar Yan Sandan jahar r SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya raba wa manema labarai.
Sanarwar ta ce Tuni kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano ya Samar da jami’an tsaro ko ta kwana domin tabbatar da bin Umarnin Gwamnatin Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jani-in-jaka tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi na biyu da kuma Sarki Aminu Ado Bayero.
Kowane bangare ya kafe kan ikirarin da yake na samun umarnin kotu da ya ba shi damar cigaba da jan ragama a inda yake.
- Tinubu ya samu tarba da sabon taken Najeriya a majalisar dokokin ƙasar
- Tinubu ya samu tarba da sabon taken Najeriya a majalisar dokokin ƙasar