Rundunar yan sandan Kano ta dauki matakan bayar da tsaro a makarantu.

Spread the love

Biyo bayan umarnin da babban sufeton yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na tabbatar da tsaro a makarantu karkashin shirin ( Safe Schools Initiative ) don kare rayuka da dukiyoyin alúmma, musamman ma na kan bayar da tsaro ga dalibai a makarantunsu.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana matakan kariyar da rundunar ta dauka domin bayar da cikakken tsaro na kare daliban a makaratunsu.

Ta cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya fitar ya ce , CP Gumel, ya umarci kwamandojin yan sanda da Baturen yan sanda , su kara kaimi wajen yin sitiri a lungu da sako na makarantun Primary, Secondary da kuma makarantun gaba da Secondary a jahar.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed usaini Gumel, ya ce hakan na nufin bayar da tsaro ga Dalibai, Malamai da ma’aikata don bunkasa ilimi a fadin jahar Kan.

Haka zalika ya kara da cewa za a kara yawan jami’an yan sanda domin dakile aikata laifuka don ci gaba da samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa mai kyau.

SCHOOLS PROTECTION: CP GUMEL DIRECTS OPERATIONAL COMMANDERS, DPOs TO ESCALATE PATROL TO PRIMARY, SECONDARY SCHOOLS, AND TERTIARY INSTITUTIONS

Yadda ‘kisan’ matashi ya janyo ƙone-ƙone a kasuwar Wuse

kwamishinan yan sandan ya yi kira ga al’umma musamman ma’aikata, Malamai, Dalibai da Iyaye su ba wa jami’an yan sandan da sauran hukumomin tsaro hadin kai , wajen sanar da su dukkan wani abu da ba su amince da shi ba, don daukar matakin da ya dace.

A karshe CP Gumel ya godewa al’ummar jahar Kano bisa addu’o’i da kuma hadin kan da suke bayar wa a koda yaushe, inda ya bukace su da su sanar da duk wani abun zargin a ofishin yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace ko sanar da ta nambobin waya 08032419754, 08123821575, 09029292926,
Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)
Instagram: Kano State Police Command
Tiktok: Kano State Police Command.
Facebook: Kano State Police Command
Play Store, the NPF (Rescue Me)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *