Rundunar yan sandan Kano ta fara neman wani tubabben dan daba ruwa ajallo bisa wasu zarge-zarge.

Spread the love

 

CP M.U.Gumel

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa salon da rundunar ta dauko na yaki da aikata laifuka musamman ma fadan daba kwalliya ta biya kudin sabulu a fadin jahar.

Kwamishinan yan sandan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Idongari.ng a shelkwatar rundunar dake Bompai.

CP Gumel ya kara da cewa, da farko sun samu matasa 222 da suka tuba daga aikata laifukan daba musamman a kwaryar birnin Kano, ya ce yanzu yawan su ya karu zuwa 623 da suka ajiye makamansu kuma dukkansu suna ba su hadin kai.

Sai dai bayyana takaicin sa kan guda daga cikin matasan da ya karya alkawarin da ya dauka har ya koma gidan jiya, inda ya ke jagorantar matasa domin dawo da harkar dabar a sassan Kano.

CP Gumel , ya ce rundunar ta samu cikakkun bayanai kan yadda matashin yake kitsa mummunar manufa ga mazauna yankin karamar hukumar Dala.

Ana zarginsa da hada matasa dauke da makamai suna tsarotar da jama’a ta hanyar wasa wukaken a kasa ba tare da sun taba kowa ba.

Ya kara da cewa idan jama’a suka firgita suka fara gudu gida sai su sace kayan al’umma, kamar yadda suka shiga gidan wani dan kasuwa da ya dawo daga kasuwa suka karbe masa kudi sama da naira miliyan biyu da kuma Zoben yarsa.

Kwamishinan yan sandan ya ce bayan samun faruwar lamarin dakarun yan sanda, sun dukafi wajen bincike har suka samu nasarar cafke wasu daga cikin yan dabar tare da kwato zoben da suka kwata.

” wannnan tashe-tashen hankulan daba da yake so ya dawo a Dala shi ne ya ke jagorantar su” CP Gumel.

Muhammed Gumel, ya kara da cewa yanzu babu batun yin yafiya tsakanin su dashi, domin sun baza komar neman sa ruwa a jallo dan ya fuskanci hukunci.

A karshe ya tabbatar da cewa sun sanya ido akansa har sai sun kama shi , kuma al’uma su ci gaba da gudanar da harkokin su kamar yadda aka saba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *