Rundunar yan sandan jihar Kano ta fitar da wasu sabbin matakan tsaro a watan azumin Ramadan, a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Kadaura24 ta rawaito Rundunar ta samar da tsare-tsare na tsaro domin tabbatar da an gudanar da azumin watan Ramadan cikin lumana da nasara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yansanda ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.
Ga shawarwarin da rundunar ta baiwa al’ummar Kano.
Masu zuwa Sallar Assham su kauracewa daukar abubuwan da bai zama dole ba, amma ba laifi su tafi da daddumar (Sallah) don rage zargi.
Ya kamata mutanen da ke halartar Masallatan da ake gudanar da Tafsiri su yi taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton duk wani abu ko motsin da ba su aminta da shi ba ga jami’an tsaro.
– Dole ne masu ababen hawa su bi ka’idojin tuki, da guje wa tukin ganganci, don kaucewa hatsari.
– An haramta wa yara ƙanana da marasa lasisi tuka ababen hawa, da suka hadar da motoci, babura da adaidaita sahu.
- Yan Sanda Sun Gurfanar Da Mutane 2 Bisa Zargin Satar Motoci A Kano
- Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara
– A kwai bukatar Iyaye su rika raka ’ya’yansu ko hada su da manya a duk inda za su shiga a lokacin azumi don gudun bacewar yaran da hadurra.
– An kuma haramta Hawan doki ba bisa ka’ida ba, an hana yin taruka wadanda ba a nemi izini ba.
– An haramta amfani da wasa da wuta ko buga wani abu mai kara a lokacin watan na Radaman.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi gargadin cewa ba za a amince da duk wani nau’in daba a cikin wata mai alfarma ba. Kuma duk wani mutum ko kungiyar da aka samu tana irin wadannan ayyuka za a dauki Matakan ladabtarwa akan su bisa doka.
Rundunar ta shawarci jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaron da suka hada da hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, jami’an tsaron farin kaya, KAROTA, Hisbah, kungiyar ‘yan Vigillante, da sauran jami’an tsaron sa kai m
Rundunar ta bukaci al’ummar Kano da su kai rahoton duk wani abu da basu yarda da shi ba ta hanyar kiran wadannan lambobin 08032419754, 08123821575, 09029292926.