Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gano Shirin Yin Kone-kone Cikin Dare A Wasu Muhimman Wurare Don Haifar Da Rudani.

Spread the love

Rundunar ta yan sandan jahar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron jahar , sun gano yunkurin da wasu batagarin Mutane ke Yi, na bankawa majalissar dokokin jahar Kano wuta da sauran wurare don tayar da hankali al’ummar jahar.

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Daren Lahadin nan.

CP Muhammed Gumel, ya bayar da tabbatacin cewar al’umma su kwantar da hankulan su, kuma su ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka Saba, domin sun baza jami’an tsaron su a sassa daban-daban na jahar.

Kwamishinan ya Kara da cewa rohotannin da Suka Samu shi ne, kan yadda wasu bakin haure ke son tayar da hatsaniya da kuma kone-konen Tayoyi don su hana al’umma zaman lafiya.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da dambarwar rushe masarautun Kano, da gwamnan jahar Kano Engineer Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe masarautar , Rano, Karaye, Bichi da kuma Gaya , a Ranar Alhamis din da ta gabata.

Danbarwar masarautar Kanon , ta bar baya da kura, tsakanin sarki na 15 Aminu Ado Bayero , Wanda gwamnan Kanon ya cire daga kujerrasa ta sarauta, inda ya zabi sabon sarkin na 16 Muhammed Sanusi na ii.

Kwamishinan yan sandan Ya kuma gargadi iyaye da shugabanni , su jawa yayan su kunne , don kaucewa dukkan wani Abu zai iya harfar da rudani ko rashin zaman lafiya, don duk Wanda Suka Kama za su Gurfanar da shi a gaban kotu.

Jaridar idongari.ng, ta kawo mu Ku yadda wasu Matasa a cikin birnin da Gaya, Bichi da kuma Rano Suka fito Suka Yi zanga-zangar nuna rashin amince wa da rushe masarautun, harma a wasu wurare a ka kona tayoyi.

” Ina so mu tunatar da Ku cewa duk Wanda ya fito da niyyar tayar da rigingimu ba za mu bar shi ba” CP GUMEL “.

Ya Kara da cewa shekara daya kenan jahar Kano, ta na cikin zaman lafiya, bayan samun nasarar magance matsalar Daba da kuma kwacen wayoyin al’umma, amma yanzu haka wasu marasa kishin zaman lafiyan da Kano ta ke dashi, na yunkurin haifar da rudani.

Sauran wuraren da ake zargin an shirya kunna wa wuta, kamar yadda wata majiya ta shaida wa jaridar idongari.ng, sun hada da , Iyaka Road, Kofar Na’isa, Kofar Nasarawa, Airport Road da kuma gidajen wasu kososhin gwamnatin jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *