Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gurfanar Da Ma Su Aikata laifuka 1,164 Cikin Kwanaki 85.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta Gurfanar da mutane 1,164 cikin kwanaki 85, wadanda Ake Zargi da aikata laifuka mabam-banta a fadin jahar.

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ne ya bayyana hakan, lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin babban sufeton Yan Sandan Nigeria, Mai lura da shiya ta daya Zone One Kano, AIG Ari Ali Muhammed, a ranar Alhamis.

Kwamishinan yan Sandan, ya shaida wa AIG Ari Muhammed, cewar Kano ta na da yawan mutane fiye da Miliyan 20, kuma ta yo iyaka da jahohin, Kaduna, Katsina, Bauchi da kuma Jigawa, kuma sun dauki matakan dakile shigowar Batagari cikin jahar , tunda ya fara Aiki a ranar 24 ga watan Yuni 2024, zuwa yanzu kuma an samu raguwar aikata laifuka.

Salman Dogo, ya kuma ce Rundunar Yan Sandan Kano, an Samar da a shekarar 1961 kuma ta na ofisoshin baturen Yan Sanda 78, area commands 11 da kuma Rundunar kwantar da tarzoma guda 2.

Kwamishinan ya bayyana damuwarsa kan yadda ya samu jahar Kano, cikin harkar daba, kwacen wayoyi, Fashi da makami da kuma ricikin masarautar Kano.

Rundunar Yan Sandan jahar, ta kama wadanda ake Zargi da aikata laifukan Fashi da makami 41, ma su Garkuwa da mutane 5, barayi 13, Dilolin kwaya 10, Yan Damfara 7, Barayin Babura 14, Yan Daba 153.

Haka zalika an kama ma su fashin wayoyin al’umma 26, Barayin motoci 11, ma su Safarar mutane 2 da kuma mutane 882 da ake Zargin sun barnata dukiya da tayar da hankulan al’umma lokacin Zanga -zangar matsin rayuwa ta watan Augusta 2024.

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya ce sun samu nasarar kubutar da mutane 5 da aka Yi Garkuwa da su da kuma tseratar da wadanda aka Yunkurin Safarar su zuwa kasashen ketare su 13.

Rundunar ta kwato bindigu, harsasai, motoci 15 , baturan Sola 17, Wukake 71, Exol, Tramadol, Sinki-sinki na tabar Wiwi 132.

Sannan an kwato Shanun sata 5, Jakuna 4 , Tumaki 15, ATM 20, wayoyi 126 da kuma Miliyoyin kudade.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *