Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar Kama wani mutum mai Suna Magaji Yallo, Mazaunin Kunya a Karamar Minjibir da jahar, Wanda ake nema kusan shekaru shida, bisa zargin sa da hannu a kisan wani matashi , Gausu Umar Sadau.
Mai magana da yawun rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wani faifen murya da ya aike wa da idongari.ng, a Ranar Alhamis din da ta gaba ta.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce sun samu Korafi daga dan uwan marigayin, tun a Ranar 10 ga watan Augustan 2018, da cewar an kashe mu Su dan uwa , inda ya yi zargin cewar wasu ne Suka Kira shi don yaje ya karbi kudinsa amma sai aka tsinci gawarsa.
Rundunar yan sandan ta Kara da cewa tun Bayan da Suka karbi korafin suka Fara gudanar da bincike, Wanda yanzu haka an Kama daya daga cikin wadanda ake zargin.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa Wanda ake zargin ya na Babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan kisan Kai dake shelkwatar rundunar a unguwar Bompai Kano, kuma tuni an gurfanar da shi a gaban kotu.
Saurari Karin Hasken Da Kakakin Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna ya yi wa Idongari.ng, bayan gana wa da dan uwan marigayin.
Daya daga cikin yan uwan mamacin Muhammed Da’i Umar, ya yaba wa rundunar Yan Sandan jahar Kano, bisa kokarin da suka yi na kamo daya daga cikin wadanda ake zargin.
Muhammed Da’i , ya Kara da cewa sun yi kiran sa ne don ya karbi kudin Babur dinsa, naira dubu 270 a garin Wailare, amma ba a bashi kudin ba, inda ake zargin Magaji Yallo, Nasiru Maigadi da Sunusi har suka daddatsashi da Gatari .
” gaskiya munji dadi shi yasa muka mu yi wa yan sandan jahar Kano, godiya da kuma jinjina mu Su , mu dai fatan mu shi ne Allah ya saka da alkairi , Allah ya Kara matsayi na gaba”Muhammed Da’i.
Yan uwan marigayin sun bukaci kotu ta yi mu Su adalci idan an gurfanar da Wanda ake zargin a gaban ta.
A karshe kakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ja hankalin al’umma don Su gane menene aikin dan Sandan , tare da cewar dukkan korafin da aka gabatar mu Su baya tsufa domin Suna gudanar da binciken kwaf har a kamo wadanda ake zargi da aikata laifuka.
” yan zu haka an gurfanar da shi a gaban kotun majistiri mai 34, dake Unguwar NormanSland , don ya zama izina ga yan baya” SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.