Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gurfanar Yan Daba 104 Da Aka Cafke A Bukukuwan Sallah.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano ta gurfanar da wasu Yan Daba 104, da aka samu nasarar cafke wa lokutan Bukukuwan karamar sallah.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifen Murya da ya aike wa da jaridar idongari.ng, da yammacin ranar Laraba.

Rundunar Yan Sandan ta kama wadanda ake zargin, a masarautun Kano guda biyar , daga Ranar 10 ga watan Afrilu 2024 da aka gudanar da Hawan Eid, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da kuma Hawan Panisau.

An gurfanar da su ne a gaban kotunan Majistiri ma su Lamba 25, 41 da kuma 70 a Jahar .

Wannan na zuwa ne bayan umarnin da kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayar don zurfafa bincike kan zargin da ake Yi mu su.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa an samu muggan makamai daban-daban da kayan maye.

Nasarar dai na zuwa ne sakamakon tsaurara matakan tsaro da rundunar Yan Sandan Jahar Kano, ta Yi a lokutan Bukukuwan karamar sallah ,inda aka kammala cikin kwanciyar hankali da lumana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *