Rundunar Yan Sandan Kano Ta Hana Gudanar Da Nau’ikan Hawan Babbar Sallah.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta hana gudanar dukkan nau’ikan hawan Sallah biyo bayan ganawa da shugabannin gamayyar hukumomin tsaro da kuma masu ruwa da tsaki, don tabbatar Tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Ranar Alhamis.

Sanarwar ta taya al’umma fatan alkairi dangane da shirin bikin babbar sallaar.

Haka zalika rundunar Yan sandan ta Kara da cewa ta Yi duk shirin da ya kamata don inganta harkar tsaro a fadin jahar.

“Wannan hanin ya biyo bayan tabbatar da Tsaro da rundunar Yan Sandan jahar Kano, tare da sauran gamayyar jami’an tsaro suka yi.” SP ABDULLAHI Kiyawa “.

Rundunar Yan Sandan ta ce an Hana dukkan hawan babbar sallah a fadin jahar Kano, bisa samun rahotanni akan abunda ya shafi harkar tsaro.

Sannan an Yi Kira ga al’umma da suje suyi sallar idi ,kamar yadda aka Saba Yi abaya.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya nemi hadin kan al’umma da kuma goyon bayan su, tare da sanar da su duk wani abu da suka gani Wanda ba su amince da shi ba , don daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *