Rundunar yan sandan Kano ta kaddamar da kwamitin mutane 11 na dokokin aikin yan sanda (Force Order 20).

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta kaddamar da kwamitin mutane 11 na dokokin aikin yan sanda (Force Order 20), domin kiyaye hakkin dan kasa ga duk wanda ya shiga hannun jami’an yan sanda , da sunan ya aikata laifi ko wanda ake gudanar da bincike akansa da kuma wanda yake tsere.

Kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa Idongari.ng, karin haske a birnin Kano.

CP Muhammed Gumel, ya ce ,sanin kowane gwamnatin tarayya ta bayar da umarni ga babban Sufeton yan sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu Agbetukun, don gyara aikin dan sandan Nijeriya, inda shugaban Yan sandan ya zauna da manyan jami’an rundnar ,tare da tsara yadda za a fitar da dokar ta hanyoyin da sukafi da cewa ga mutanen Nijeriya, karkakashin jagorancin ma’aikatar shari’a ta kasa , domin ya kasance kundin laifukan tuhume-tuhume na ACJL, ana bin ka’idojin sa ,wajen kiyaye hakkokin kowanne dan Nijeriya da ya shiga hannun yan sanda.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa mukaddashin kwamishinan yan sandan jahar Kano, DCP A.A. Shika, daga sashin binciken sirri na rundunar , shi ne zai jagorancin kwamitin.

Mambobin kwamitin karbar shawarwarin da aka kaddamar ya kunshi, Daraktan aiyuka na musamman na fadar gwamnatin jahar Kano, Ministan shari’a na kasa , kwamishinan shari’a na jahar Kano, Babbar mai shari’a ta jahar Kano, Alkalan babbar kotunan jahar Kano, shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da hana cin hanci da rashawa na jahar Kano.

Ƴansanda a Anambra na neman wani sufeta ruwa a jallo kan zargin kisa

Muna son a yi sasanci kan ficewar kasashen Sahel daga Ecowas – Yan farar hula

Sauran yan kwamitin sun hada da shugaban kungiyar lauyoyi na Kano, Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa, Lauyoyi, NOA, Hukumar aiyukan yan sanda PSC, NYSC, da kuma hukumar gidan gyaran hali da tarbiya.

A karshe CP Gume, ya ce dukkan mutane sha dayan za su kasance Manbobin kwamitin, kuma za su dinga tuntubarsu domin karbar shawarwari.

Daraktan hukumar wayar da kai ta kasa reshen jahar Kano NOA, Alhaji Salisu Waziri Kutama, ya bayyana cewar hakika kaddamar da kwmaitin zai kawo sauyi nan bada jimawa ba, kasancewar an zakulo wadanda za su tabbatar an gudanar da komai bisa ka’idar doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *