Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Kwayoyi Na Sama Da Naira Miliyan 80

Spread the love

 

 

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samau nasarar kama kwayar tramadol wadda kudinta ya kai sama da naira miliyan tamanin da biyu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, a ranar asabar.

Yanzu haka wanda ake zargin mai suna Usman Umar yana hannun jami’an yan sandan , inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

A cewar Kiyawa, “Mun sami sahihin bayanai kan cewar an ajiye wata mota da ake zargin tana ɗauke da miyagun ƙwayoyi a unguwar Rimin Auzinawa, kuma nan take jami’anmu suka bi sawun motar zuwa cikin unguwar, bayan sun kewaye gidan da aka ajiye motar sai suka kama wani matashi mai suna Usman Umar, a gidan tare da gano kayan Mayen”.

Kayan Mayen da aka gano sun hadar Fakiti 603 na ƙwayar Tramadol me ɗauke da ƙwayoyi 60,300, da kudinsu ya kai ₦60,300,000, sai Fakiti 299 na Pregabalin me ɗauke ƙwayoyi 44,850 da kudinsu ya kai ₦22,425,000, wanda jimillar kimar kudin kayan Mayen ya kai ₦82,725,000.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar bisa goyon baya da hadin kai suke bayar wa wajen samun nasara.

Haka kuma ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *