Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Mutane 2,425 Da Zargin Aikata Laifuka A Shekarar 2024

Spread the love

 

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da aikata laifuka 2,425 tare da kwato muggan makamai, kwayoyi da kuma kayan sata daga ranar 1 ga watan janairu zuwa Disamban 2024.

kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yin karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a shekarar da muke bankwana da ita.
CP Dogo, ya ce a farkon shekarar 2024, an yi fama da yunkurin yan bindiga na shigowa jahar wanda suke da kananan hukumomi 17 akan iyakokin jahohin, Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi.

Haka zalika akwai kuma barazanar fadan daba da kuma masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a kananan hukumomin 8 na kwaryar birnin Kano.

Sai kananan hukumomi 19 wadanda basa cikin birni ko kan iyaka , da aka samu yawan sace-sace da fada tsakanin makiyaya da manoma.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa, kamar yadda babban sufeton yan sandan Nigeria, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ba da umarni tare da sanya su a kan hanya don ganin an fadada bada tsaro, a Nigeria gaba daya wadanda suma a jahar kano ba a barsu a baya ba, inda suka kalli matsalar jahar, har suka dauki matakan magance matsalar musamman wajen kara inganta aikin tsaro da al’umma da bibiya a duk lokacin da suka samu bayanan sirri na yunkurin shigowar yan ta’adda suna kai daukin gaggawa tare da sauran gamayyar hukumomin tsaro.

Ya ce an kuma sake karfafa tattara bayanan sirri da kara fadada sintiri a lungu da sako , don tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’ummar jahar.

Cikin nasarorin da rundunar ta samu sun hada da cafke yan fashi da makami 189, masu garkuwa da mutane 34, barayin shanu 10, masu safarar bindigu 2, barayin motoci 22, dilolin kwaya 58, masu fasa kaurin mutane 18, barayin adaidaita sahu 46 da kuma barayin babura 28.

Sannan an cafke masu buga takaddun bogi 4, yan damfara 27 da kuma yan daba 1987.

CP Salman Ya ce sun tseratar da mutane 40 da aka yi safararsu da kuma kubutar da mutane 18 wadanda aka yi garkuwa da su , sai mutane 2 da aka sace.

Haka zalika rundunar ta kwato bindiga kirar AK-47 guda 7, Beretta Pistol 1, Pump Action 4, Bindigar harbin tsintsaye 7, kirar gida 4 da kuma bindigar wasan yara 4.

Sannan an kwato harsasai 1,213, Adduna 57, Wukake 198, motoci 12, babura 44, adaidaita sahu 15, kudin jabu naira biliyan 129 da miliyan 542 da dubu 823 na kudaden katare da kuma na Nigeria.

An kwato shanun sata 308, ATM Card 65, wayoyin sata 415, zoben azurfa 67, baturan sola 34 da kuma allurar 105.

A karshe rundunar ta godewa gwamnatin jahar Kano, sauran hukumomin tsaro, kungiyoyin al’umma, yan sandan kwansitabulari, yan bijilanti , PCRC da kuma kafafen yada labarai da wakilansu bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a musamman akan abunda ya shafi tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *