Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Mutane 41 Da Makamai, Kayan Maye Bisa Zargin Addabar Jama’a.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta kama mutane 41 da ake Zargi da addabar jama’a, sassan jahar.

Wannan ya biyo bayan rahotannin da Rundunar Yan Sandan ta samu kan yadda batagarin suke zama tare da addabar mutane.

Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya bayar umarnin shiga wuraren tare kama mutane 41 da kuma makamai da kayan maye da aka samu a wajensu.

Kwamishinan yan Sandan ya godewa al’ummar jahar Kano, bisa hadin kan da suke bayarwa domin duk irin wani laifi da ake aikata wa a jahar Yana raguwa.

Kakakin Yan Sandan Kano SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa daman tuni babban sufeton Yan Sandan Nigeria AGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarnin Fadada Sintiri da kuma tabbatar da amfani da bayanan sirri domin inganta tsaro.

Rundunar Yan Sandan jahar Kano karkashin jagorancin CP Salman Dogo Garba, ta yi babbar nasarar magance matsaloli na tsaro, Inda aka gudanar da Sintiri a lungu da sako na kwaryar birnin Kano, tare da Kai sumame a wuraren da ake Zargin batagarin matasa suna aika-aika a wuraren.

Sumamen ya Kai ga cafke mutane 41 da makamai da kuma kayan mayen da suke sha suna buguwa.

Wannan ya biyo bayan dagewar da Rundunar Yan Sandan ta yi, domin ganin an tabbatar da tsaro a Kano gaba daya.

Haka zalika Rundunar Yan Sandan ta kara godewa al’umma , saboda an samu raguwar aikata laifuka a wannan lokaci da ake ciki.

CP Dogo Garba, ya tabbatar wa da al’umma cewa za su ci gaba da zage damtse na tabbatar da tsaro da kare rayuka, lafiya da kuma dukiyoyon su.

A karshe Rundunar ta Yi kiran a ci gaba da ba wa Rundunar Yan Sandan jahar Kano, hadin Kai domin ci gaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya, Inda rundunar ta bayar da nambobin Waya don sanar da ita wani motsi ko wani Abu da ba a amince da shi ba ko agajin gaggawa.

08032419754, 08123821575, 09029292926

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *