Rundunar yan sandan jahar Kano ta yi holen mutane 82, wadanda ake zargi da aikata laifukan, Fashi da makami, Garkuwa da mutane, Dilolin kwaya, Yan Damfara, Barayin Babura da kuma Yan Daba.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani, a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai kano a ranar Alhamis.
Rundunar ta ce al’ummar jahar Kano suna ba su hadin kai, kuma duk wanda ya fito ya ce zai aikata ta’adanci kafin kace Kwabo an cafke shi.
Idonagar.ng, ta ruwaito cewa, an samu raguwar yawan aikata laifuka a jahar, sakamakon kara hada alakar aiki da al’umma da kuma rundunar yan sandan jahar, da bibiya a lungu da sako don tattara bayanan sirri tare da kakkabe batagari.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce wannan umarni ne , na babban sufeton yan sandan Nigeria, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, kamar yadda ya bayar da umarni, don ci gaba tabbatar da zaman lafiya.
Haka zalika rundunar ta ce an samu gagarumar nasarar magance harkar Daba musamman a kananan hukumomin birnin Kano da magance abubuwan da ya danganci fashi da makami, musamman a jahohin da suke da iyaka da Jahar Jigawa da kuma Jahar Bauchi.
An kuma samu nasarar magance harkar Garkuwa da muutane, musamman a kan iyakokin Kaduna da kuma jahar Katsina.
- Hukumar Kashe Gobara Ta Bayyana Musabbabin Tashin Gobara A Kasuwar Yan Katako Brigade A Kano
- Ma’aikatar Tsaron Najeriya Ta Mika Sabbin Jiragen Saman Shelkwafta Ga Rundunar Sojin Ruwa
Wannan aikin dai an yi shi ne daga ranar 1 zuwa 14 ga watan Nuwamban 2024, inda aka kama masu aikata laifuka 82, kuma tuni an gurfanar da guda 60 a gaban kotu bisa zargin aikata laifuka mabambanta , sai dai 22 ana ci gaba da gudanar da bincike akansu kafin a gurfanar da su.
Rundunar ta kama wadanda ake zari da aikata laifukan Fashi da makami 13, Masu garkuwa da mutane 2, Dilolin kwaya 12, Barayin Babura 2, Yan Damfara 5, Yan Daba 35 da kuma barayi 13.
Haka zalika an kwato bindiga kirar AK-47 guda 1 da kuma kirar gida guda 3, Adduna 13, Wukake 16, Babura 3, Adaidaita Sahu 1, Sinkin Tabar Wiwi 24 da kuma kulli-kulli 175.
Kiyawa ya kara da cewa an samu kwayar Diazepam 50, Tramadol 42, Pregabalin Tablets 307, Madarar Sukudayin 2, Wayoyin Hannu 10 da kuma Tagogi guda 10.
Cikin wadanda aka kama din akwai wadanda ake zargi da aikata laifukan Fashi da Makami, a kananan hukumomin Gabasawa, Gezawa da kuma Wudil da kuma wani matashi da ake zargi da Damfarar yan mata da sunan ba su tallafi.
Haka zalika rundunar ta godewa gwamnan jahar Kano, Engr, Abba Kabir Yusuf , bisa bisa ba su kyautar motoci guda 78, don fadada sintiri a lungu da sako jahar.
Rundunar ta bayyana cewa zata ci gaba da wayar da kan al’umma don tabbatar da tsaro a fadin jahar.