Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Sha’aibu Abdulkadir dan shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai dake kwaryar birnin jihar, bisa zargisa da halaka wata matar aure mai suna, Rumasa’u Haruna yar shekaru 22, a gidan auren ta dake unguwar Farawa karamar hukumar Kumbotso ta jihar.
Wanda ake zargin ya shiga gidan matar auren a yankin Tsamiyar Duhuwa, a ranar 6 ga watan Afrilun 2025 inda ya yi mata kisan gilla.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke Sha’aibu Abdulkadir, ne a ranar 23 ga watan Mayun 2025, ta hanyar binciken sirri.
- An Kama Matasa 27 Da Zargin Kashe DPO Bayan Sun Farmaki Ofishinsa A Rano
- Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Da Bulala 150 Ga Wanda Aka Samu Da Laifin Kunnawa Mutane Wuta A Masallaci
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsawa jami’an yan sanda, cewa ya shiga gidan wadda ya halaka din inda ya shaketa sannan ya soka wuka, a wuya lamarin da ya yi sanadiyar rasuwarta.
Tuni matashin ya amsa aikata laifin a wajen jami’an yan sandan, wanda faruwar lamarin ya tayar da hankalin al’umma musamman a arewacin Nijeriya.
A wancan lokacin yan sanda sun garzaya da ita asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarta.
Rundunar ’yan sandan ta yaba wa jami’anta da suka gudanar da bincike saboda kwarewarsu da kuma jajircewarsu wajen cafke wanda ake zargi, inda ta kara da cewa ana ci gaba da bincike don tabbatar da an yi cikakken adalci.
A karshe rundunar yan sandan ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.