Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kammala Dashen Bishiyu 400.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta kammala dashen Bishiyu guda 400, a ofisoshin Baturen yan sanda, Kwamandojin yan sanda da kuma Barikokin Yan sanda.

Jami’in Hulda da jama’a na Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Ranar Lahadi.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce sun samu tallafin Bishiyun karkashin jagorancin Isma’il Auwal, a makon da ya gabata.

Yaka da cewa dukkan Baturen yan sanda da kuma kwamandojinsu da Kansu suka dasa Bishiyoyin, tare da alkawarin Ba su kulawar da ta dace wajen ganin an samu wadatacciyar iska sakamakon yadda ake yawan sare bishiyu Ba tare da an marar da gurbinsu ba.

Rundunar Yan Sandan ta ce dukkan Wanda yake da korafin wani ya safe masa bishiya KO kuma ta gwamnati zai iya shigar da korafin sa a ofishin yan sandan mafi kusa.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayar da jagoranci dasa Bishiyoyin, don taimakon al’umma ta kowanne bangare da za a samu ci gaban al’umma da kuma kare kwararowar Hamada kamar yadda baban sufeton Yan Sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Abegketun, ya bayar da umarni.

Tun abaya masana a bangaren Lafiya da Muhalli , ke Jan hankalin al’umma kan illar yawan sare bishiyu , inda Iska mai karfi ke rushe gidaje ma su tarin Yawa musamman a lokutan damuna da kuma sauran illolin dake faruwa ga lafiyar Muhalli da zaizayar kasa da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *