Rundunar Yan sandan Kano, Ta Karbi Shawarwari Daga Masarautun Jahar da Malaman Addini Don Bayar Da Cikakken Tsaro A Bukukuwan Sallah.

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Kano tare da sauran hukumomin tsaron jahar, sun Shirya tsaf, don tabbatar an gudanar da bukukuwan karamar Sallah lafiyarsu lafiya.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a wajen taron da aka Shirya tare da Sarakunan Kano da kuma Malamai a ranar Litinin.

CP Gumel, ya ce a matsayinsu na jami’an tsaro, suna Ci gaba da gudanar da bincike kan fargabar da ake yi , yayin gudanar da bukukuwan karamar Sallah, da zata janyo jikkata al’umma koma rasa rai baki daya.

Kwamishinan Yan sandan ya Kara da cewa, jahar Kano ce daya tilo da tafi sauran jahohin da suke makotaka da ita, samun zaman lafiya daga barazanar ma su satar Mutane da sauran muggan laifuka.

” Akan haka ne muka ce hakkin mu ne mu tabbatar wadannan mumunan Abu ba su faru ba, har muka Kira Malaman mu , Sarakunan mu don tattauna wa” CP Gumel “.

Ya kara da cewa , a zaman suka yi zai ba su damar karbar shawarwari daga guraren da ake samun barazana da kuma yadda za a dakile ta.

CP Gumel ya yaba wa Sarakunan da Malamai wajen kasancewar su tare a koda yaushe , tare da Jan hankalin matasa wajen kaucewa dabi’u marasa kyau.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa Kakakin Yan sandan Kano

Masarautun Kano guda biyar da suka hada da, Kano, Gaya, Bichi, Rano da kuma Karaye ne suka halacci taron.

A bangaren Malaman addinin da suka halacci taron tabbatar da tsaron sun hada da, Izala, Tijjaniya da Kadiriyya.

Wakilin fadar masarautar Kano, ya roki Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, ya Kara mu su yawan jami’an tsaro musamman abinda ya shafi Masallacin Idi, gidan Shattima, Masallacin Juma’ar gidan Sarki da filin Hawan Daushe.

Haka zalika ya roki rundunar, ta rufe hanyoyin da suka shafi Mahadar Kwalli, Dan’agundi, Kofar Kudu, Gwangwazo, Tudun Wuzirci, Galadanci, Kwanar Diso, Mandawari da kuma filin Kofar Mata.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce shawarwarin da aka bayar sun dauke su a rubuce, kuma za yi aiki da su.

Sannan ya tabbatar da cewa dukkan Baturen yan sandan yankunan , za su dauki matakin nan ta ke na guraren da aka lissafa.

Rundunar Yan sandan ta Ci alwashin Kama dukkan wani mai kunnen kashi, wajen tayar da hankulan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *