Rundunar Yan Sandan Kano Ta Sabunta Sashin Karbar Korafin Mutanen Da Jami’in Dan Sanda Ya Ci Zarafinsu.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, karkashin jagorancin kwamishinanta CP Salman Dogo Garba, ( Dogon Aiki) ta kara jaddadawa al’umma jahar cewar har yanzu kofa abude ta ke ga wadanda suke da korafi kan wani jami’in dan sanda da suke zargin ya ci mutuncinsu, zagi , Cuta ko kuma aikata ba daidai ba.

CP Salman Dogo , ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,( Bawahala) a wani faifen bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Facebook.

Sanarwar ta ce, daman akwai sashin karbar korafe-korafen al’ummar, sai dai an sabunta shi da kayan aiki irin na zamani kamar yadda babban sufeton yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Abegtekun, ya bayar da umarni da kuma kara yawan ma’aikata don ganin an samu kyakkyawar alaka tsakanin jama’a da yan sanda.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce aikin dan sanda aiki ne na amana kuma ana yi ne don al’umma , don haka duk wanda ya aikata daidai tun a duniya zai ga sakamako, ko kuma akasin haka.

‘’ idan mutum ya tsaya ya yi aiki akan gaskiya zai kai shi Aljanna, idan ka yi ba daidai ba tun a duniya zaka gani’’ SP Abdullahi Haruna Kiyawa’’.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa SP Muhammed A. Ahmed, ne ke jagorantar sashin karbar korafe-korafen jama’ar da suke son shigar wa kan jami’in dan sandan da aka samu ya aikata ba daidai ba.

Sashin dai yana tattara bayanan al’umma tare da bincika wa sannan a tura rundunar yan sanda ta kasa dake Abuja don daukar matakin da ya dace kan duk jami’in da aka samu da aikata ba daidai ba.

A karshe rundunar ta bayar da nambobin shigar da korafin 09134558533 ko 08115657624 ko kuma mutum ya shigar da korafin sa kai tsaye a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai Kano.

Saurari bayanin SPAbdullahi Haruna Kiyawa

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *