Rundunar yan sandan Kano ta sake ganawa da jam’iyun NNPP, APC da shugannin kananan hukumomi don mutunta yarjejeniya zaman lafiya gabanin yanke hukuncin kotun koli

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, tare da sauran hukumomin tsaro sun sake ganawa da shugabancin jam’iyar NNPP da APC , da kuma shugabannin kananan hukumomin Gezawa, Wudil da Tudunwada don ci gaba da sanya ido da kuma mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyun suka rattaba wa hannu.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Gumel, ya ce kiran shugabannin jam’iyun ya zama wajibi kasancewar akwai abubuwa guda uku da suke tunkarar su , na karshen shekara da suka hada bikin kirsimeti, bukukuwan sabuwar shekara da kuma hukuncin karshe da kotun koli zata yanke kan wanda yake shi ne  halastacen gwamnan Kano.

Gumel ya kara da cewa sun zabi kananan hukumomin Gezawa, Wudil da kuma Tudunwada, domin kananan hukumomin ne da suke kan hanyar da jama’a suke shigowa jahar Kano daga kasashe na duniya da kuma wasu bangarorin fadin Nijeriya, ya ce a kowanne lokaci suna daukar wuraren da muhimmannci don duk lokacin da aka rufe hanya koda minti daya ne  hakan zai shafi matafiya.

Ya kuma bukaci shugabannin kananan hukumomin ukun , su kira sauran takwarorin su, da kuma jami’an tsaron da suke aiki a yankunnan dan kara sanya ido kar abar bakin haure su shigo dan su tayar da hankulan jama’a.

Kwamishinan yan sandan ya ce, wannan lokaci na karshen shekara akwai bikin sabuwar shekara, kirsimeti da maganar yanke hukuncin ake saran kotun koli zata yanke kan wanda ya zai zama halastaccen gwamnan Kano.

“kowanne lokaci ko kowanne mataki ace ba ayi harkar kirsimeti yadda yakamata ba ko bikin sabuwar shekara abun kunya ne saboda wasu tsararun mutane bakin haure su tayar da hankulan jama’a”CP Gumel”.

Muhammad Gumel ya ce akwai wasu da suke yin kunle-kunle wadanda bama yan Nijeiya ba ne , harda wasu kafafen yada labarai na kasashen ketare, wadanda suke yadawa abubuwan ba daidai ba.

Ya dada yin kira kar abar wasu batagari su shigo tare da tayar da tarzoma akan wadanda ba su ji ba basu gani ba koma su rasa dukiyarsu.

Gumel ya kara da cewa a matsayin su na shugabannin tsaro, da kuma shugabannin jam’iyun da na kananan hukumimi idan suka bar wani abu mara dadi ya faru to sun bar abun kunya ne da har abada ba za a taba mantawa da su ba.

Kwamishinan ya ce tattaunar da suka yi sun amince babu wani da za su bari ayi amfani dashi domin kawo abunda zai tayar da hankali a jahar Kano kamar yadada shugabannin jam’iyin da tare da shugabannin kananan hukumomin da cewar dukkan wani batagari da ya aikata wani abu bada yawun jam’iyar NNPP da APC ba ne kawai ya yi gaban kansa ne.

Gumel ya ce za su bi dukkan wanda ya aikata wani abu su kamoshi dan hukunta shi kamar yadda doka ta basu dama.

Shugabannin jam’iyun da na kananan hukumomin sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu tare goyon bayan wanzar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *