Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta tabbatar cewa yanzu haka, jami’an ta 2 ne suke kwance a asibiti, Inda aka sallami 9 daga cikinsu bayan mummunan Hatsarin da ya rutsa da su a hanyarsu ta dawo wa daga wani Aiki na musamman.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Lahadi 29 ga watan Satumba 2024.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce bisa rahotannin da suka samu , shi ne Wani Mai babbar mota ce da ya Yi Lodin don Sauke su a jahar Kano, Amma da Zuwan sa Kwanar Dangoro sai ya sauka daga motar , ya ba wa yaron motarsa Tukin don ya kawo kayan cikin Garin Kano.
Ya kara da cewa yaron direban ya tuko motar akan Titin Zaria zuwa Kano, Inda ya tsaya a Garin Karfi dake karamar hukumar Kura, ya Sauke kaya a cikin Wani lungu da Ba zai iya yin Kwana ba, inda ya yanke shawarar yin Ribas har Zuwa kan Titin zuwa Zaria.
Duk da cewa yaron motar ya ce wasu suna duba masa kan titin Amma ta dinga tafiya da baya, Inda motar da Yan Sandan suke ciki ta ke kokarin kaucewa Tilerar kasancewar cikin dare ne har ya Faru.
Yan Sandan 16 ne a cikin motar, Inda 5 suka rasu sannan 11 suka samu raunuka , kuma tuni aka sallamo 9 daga cikinsu.
Yanzu haka ragowar biyun da suka rage , Daya Yana kwance a asibitin Kwararru na Murtala Muhammed Kano, dayan kuma a asibitin karamar hukumar Bichi.
” Dole a Yi alhinin abun saboda an rasa jajirtattun matasa wajen gudanar da aikinsu , hatta Yan uwansu da abokansu suna ta fadar cewar mutanen kirki ne” SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.
Yanzu haka dai yaron motar ya na Hannun Rundunar Yan Sandan jahar Kano da kuma motar, Inda rahotanni suka Bayyana cewa Direban motar da ya sauka a Kwanar Dangoro ya gudu dajin labarin abunda ya Faru.
Rundunar Yan Sandan ta ce za ta Gurfanar da yaron motar a gaban Kotu, har ta Yi kira ga Direban da ya gudu ya mika Kansa wajen jami’an Yan Sanda.