Rundunar yan sandan jahar Kano, bisa jagorancin kwamishinan ta, CP Muhammed Usaini Gumel, ta fara gudanar gangamin wayar da kan al’umma, a kasuwanni, tashoshin mota da dai sauransu, don ilimantar da su kan hanyoyi da za su bi wajen shigar da korafin su, idan wani jami’in dan sanda ya yi mu su ba daidai ba.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari.ng, da yammacin ranar Alhamis.
SP Kiyawa ya ce zagayen na kwanaki biyu ne, wanda aka fara daga ranar Alhamis 21 ga watan Maris zuwa ranar juma’a 22 ga watan maris 2024.
Wannan dai na zuwa ne bayan rundunar yan sandan jahar Kano, ta gano cewar akwai mutane ma su tarin yawa da suke da korafe-korafe kan yan sanda amma babu hanyar da za su shigar da korafinsu.
Hakan ya sanya an gana da al’umma da suka hada da, Yan kasuwa, masu Ababen hawa da kuma mutanen gari, don tsaftace aiyukan yan sandan wajen yin gaskiya, rikon amana da bin doka da oda, wajen daukar mataki kan dukkan wani jami’in dan sanda da aka samu da yin ba daidai ba.
Ya kara da cewa, akwai tsare-tsare da babban sufeton yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Abegtokun, ya bayar da umarni don tabbatar da anyi aiki na kwarai.
Kiyawa ya ce, zagayen ya kara kulla alaka tsakanin al’umma da jami’an yan sandan, wajen sanin hanyoyin da za su bi, su shigar da korafinsu kan wani jami’in dan sanda ko neman daukin gaggawa.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi kira ga al’umma da su yi amfani da wannan damar wajen bayar da rahotannin abubuwan da zai taimaki tsaron jahar, da kuma bayar da rahotan dan sandan da ya yi mu su ba daidai ba, don ganin an yi gyaran da yakama ta.
CBN ya ce ya kammala biyan bashin dalolin Amurka da suka maƙale a hannunsa
Yan Sandan Kaduna Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Satar Wayar Wutar Lantarki.
Kasuwannin da rundunar yan sandan jahar Kano, ta zagaya sun hada da kasuwar Sabongari, Kwari, Singa, Malam Kato da kuma tashoshin matar, Unguwa Uku, Kano Line da filin Fakin kamar yadda jaridar Idongari.ng, ta ruwaito.
Al’ummar da rundunar yan sandan, ta ziyarta a wajen kasuwancinsu, sun bayyana farin cikinsu, tare da yin alkawarin bayar da cikakken hadin kai ga rundunar.
Kakakin yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar a shirye ta ke wajen daukar mataki mai tsauri ga duk wanda ya yi yunkurin kawo wa rundunuar cikas a aiyukan da ta ke gudanarwa.
A karshe rundunar ta bayar da Lambobin waya na kar ta kwana domin shigar da korafi ko neman daukin gaggawa.
08032419754, 08123821575,09029292926, 091345533 da 08115657624.