Rundunar yan sandan jihar Kano, ta na neman iyayen wani yaro mai suna Abulkhair dan shekaru 6 a duniya, wanda aka tsinke shi a Airport Road Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafin sa facebook, ya ce ga duk wanda ya san yaron su zo shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai ofishin kakakin rundunar.
Rundunar ta ce tun a ranar 21 ga watan Febarairun 2025 , aka tsinkeshi kuma an yi kokarin da yakamata don mayar dashi hannun iyayensa amma ba a samu ba.
A karshe rundunar ta bayar da nambar waya don neman Karin bayani kamar haka 07033093437 da kuma 09029893668 Allah ya sa adace amin
- Hukumar Karota Ta Yi Kira Ga Direbobi Da Su Yi Tuki Cikin Hankali A Watan Ramadan
- An Umarci Masu Gidajen Rawar Gala Da Wasanni Su Rufe A Kano