Rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da kama maza da mata su 29, daga garuruwa 2 da suka yi fada akan Awarar naira 300.

Spread the love
SP Abdullahi Haruna Kiyawa Kakakin yan sandan Kano

Rundunar yan sandan jahar Kano , ta tabbatar faruwar wani fada da ya barke tsakanin mutanen garuruwan Tukwi da kuma Keɓa, a karamar hukumar Makoɗa dake jahar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna , ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifan murya da ya aike wa Idongari.ng, da yammacin ranar Alhamis.

Kiyawa ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 3 ga watan Janairun 2024, tsakanin garuruwan biyu, inda wani matashi ya tsallaka garin Tukwi domin siyan Awara ta naira 300 a wajen wata yarinya har ake zargin ya karbi Awarar amma bai biya ta kudin ba.

Ya kara da cewa hakan ne ya sanya matasan yankunnan biyu suka yi fada tare da jiwa wasu raunuka har sai da manyan yankunan suka lamarin.

SP Abdullahi Haruna ya ce kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayar da umarnin kai daukin gaggawa zuwa garuruwan biyu, tare cafke mutane 29 wadanda suka hada da maza 27 da mata 2.

Matashin da ake zargi da janyo fadan sakamakon rashin biyan kudin Awarar Nasiru Abdullahi Keɓa, ya bayyana cewa ya siyi awarar ta naira dari uku a wajen ta ,kuma ya bata naira 500 amma sai ta ce masa bata da chanji.

Matashin ya kara da cewa ya bukaci ta bashi domin ya samo chanjin saboda sauri yake yi, sai dai ta bayyana masa cewa guduwa zai yi da kudin nata ba zata bashi dari biyar din ba.

Bayan haka sai daya daga cikin matasan garin Tukwi , ya zo tare da tambayar abunda ya faru , har sauran matasan suka dauko Katako suka rufe shi da duka saboda ya ce sauri yake yi.

Shima Hamisu Idris Tukwi , da ake zargin daga cikin matasan da suka rufe matashin da duka , ya bayyana cewa irin wannan fadan ya faru karo na uku kenan tun tasowarsa amma wannan yafi munana.

Ya kara da cewa tun a ranar da lamarin ya faru suka shata layi tsakanin su , da yan garin Keɓa da cewar karsu kara tsallako mu su gari yin siyayyar kayayyaki kowa ya tsaya a garinsu.

Yanzu haka dai rundunar yan sandan Kano, ta ce an dawo da batun zuwa babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka dake Bompai tare da ganawa da manyan garuruwan biyu dan warware tsabanin dake tsakaninsu tun daga tushe.

IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *