Rundunar yan sandan jahar Kano, ta tabbatar da rasuwar jami’an ta guda 5 , ya yin da wasu 10 suka samu raunuka a wani mummuna da ya rutsa da su, a yankin karamar hukumar Kura dake jahar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ( Bawahala) ne ya bayyana hakan ga jaridar idongari.ng, a ranar Talata.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce a daren jiya suka samu rahotan faruwar hadarin a lokacin da jami’an yan sandan, suka dawo daga aikin da aka tura su , jahar Edo, inda wata Tirela ta ke yin ribas ba tare da sanya wata alama ba.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa rundunar ta nuna alhini tare da mika sakon ta’aziyarta ga iyalan wadanda suka rasu, da kuma yi mu su addu’ar samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka.
Itama hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jahar Kano, CRC Abdullahi Labaran, a madadin kwamandan hukumar Tijjani Mohammed, ya bayyana alhini da jimami, inda ya mika sakon ta’aziyarsa ga rundunar yan sandan jahar Kano da kuma iyalan wandand iftila’in ya faru da su.
- Lokaci ya yi da za a daina biyan tallafin man fetur a Najeriya – Dangote
- Na yi da-na-sanin rashin sayan Arsenal – Dangote