Yan Sanda Sun Yi Holen Matasa 24 A Kano Kan Zargin Fadace-fadacen Unguwanni

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar kama mutane 24, wadanda dukkansu matasa ne dauke da muggan makamai bisa zarginsu da yin fada unguwanni.

 

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta ce an samu nasarar kama matasan ne biyo bayan fadace-fadacen da ya faru tsakanin Kafar Mata, yakasai, Zango , Zage da kuma sauran makotan unguwanni , daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Disamban 2024.

A ranar 13 zuwa 16 ga watan da muke ciki kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya tura dakarun yan sanda zuwa sassan wuraren da lamarin faru tare da bibiyar halin da ake ciki har aka samu nasarar cafke matsan da ake zargi dauke da mugan makamai.
Rundunar yan sandan ta byaar da nambobin kiran gaggawa
– 08032419754
– 08123821575
– 09029292926.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *