Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama waɗanda ake zargi ɓatagari ne su 89 har da masu fashi da makami 15 da wasu mutum 10 da ake zargi dilolin miyagun ƙwayoyi ne da kuma mutum guda da ake zargi mai safarar mutane ne.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce jami’an ƴan sanda sun samu nasarar kuɓutar da mutum biyu da aka yi safararsu da ƙarin biyu da suka tsinci kansu a hannun masu garkuwa da mutane.
SP Kiyawa ya ƙara da cewa rundunar ƴan sandan ta kuma ƙwato haramtattun miyagun ƙwayoyi da muggan makamai da kuma muhimman takardu da aka sace har da kwalabe 538 na maganin Bacardi da kuma ƙunshin busassun ganyayyaki da ake zargi tabar wiwi ce.
Sanarwar ta ce rundunar ta gudanar da waɗannan ayyukan ne tsakanin 12 da 30 ga watan Satumban bana.
Kiyawa ya bayyana cewa dabarun da jami’an rundunar ta ɗauka ne ya kai ga nasarorin inda kuma tuni aka tisa ƙeyar mutum 43 da ake tuhuma zuwa kotu yayin da ake gudanar da bincike a kan wasu 46.
Kakakin rundunar ya kuma bayar da tabbaci cewa rundunarsu ta kammala dukkan matakan tsaron da suka dace yayi da kuma bayan bikin ranar ƴancin kai da za a yi gobe, Talata.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Sake Yin Karin Haske Kan Hatsarin Da Ya Rutsa Da Jami’an Ta.
- Kotu Ta Yanke Matashin Da Aka Samu Da Laifin Kai Wa Mara Lafiya Kwayoyi A Gadon Asibiti Hukunci.