Rundunar Yan Sandan Kano Ta Yi Holen Mutane 92 Bisa Zargin Aikata Fashi Da Makamai, Garkuwa, Damfara Da Fadan Daba.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta cafke mutane 92 da ake zarginsu da aikata laifuka mabambanta, a cikin makonni uku da suka gabata.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan , a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a ranar Litinin.

Wadanda ake zargin sun hada da masu garkuwa da mutane, yan fashi da makami, barayin ababen hawa da kuma yan daba cikinsu harda marigayi Abba Burakita da rundunar ta ke nema ruwa a jallo , bisa zargin aikata fashi da makami.

SP Kiyawa, ya ce wannan nasarar ta samu bisa jajircewar jami’ansu na nuna kwarewa don tabbatar da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.

Rundunar ta kama wadanda ake zargi da aikata fashi su 16, masu garkuwa da mutane 3, barayi 7, Dilolin kwaya 6, yan Damfara 7,Barayin motoci 6 da kuma yan Daba 47.

Wakilin idongari.ng, ya ruwaito cewa rundunar ta kwato Mota guda 1 da ake zargin ta sata ce, bindiga kirar gida 1, baturan Sola 5, Wukake 41, Exol tablet 298, Tramadol 12, Diazepam 2 da kuma sinki-sinki na tabar wiwi 55.

Sauran kayyayakin sune baburan Adaidaita sahu 2, babura 12, keken dinki 1, ATM guda 20da jabun kudi naira dubu dari biyu da arba’in da daya da kuma kudi sama da naira miliyan ashirin da daya.

Rundunar ta godewa al’ummar jahar bisa hadin kai da goyon bayan da suke ba ta a koda yaushe.

Abdullahi HarunK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *