Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta yi bikin kara wa jami’an ta 272 girma, a matakai daban-daban kamar yadda hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa PSC ta amince.
An gudanar da bikin karin girman a wajen shakatawar manyan jami’an yan Sanda dake unguwar Bompai a ranar Litinin.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya taya wadanda suka samu karin girman, Inda yaja hankalin su kan ci gaba da jajircewa kan aikinsu.
Cikin wadanda likafar ta su ta daga sun hada da, mataimakan kwamishinan yan sanda 4, sai mutane 50 daga matakin SP zuwa CSP sai mutane 32 daga DSP matakin zuwa SP da kuma mutane 186 daga matakin ASP zuwa DSP.
Rundunar ta ce wannan rana ce ta farin ciki agare su, da wadanda suka samu karin girman da kuma iyalansu.
- Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, Ya Taya Gwamna Yusuf Murnar Cika Shekaru 62, Ya Bayyana Shi A Matsayin Shugaba Mai Hange.
- Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ake Zargi Da Yin Garkuwa Da Yaro Sannan Ya Nemi Kudin Fansar Miliyan 50 A Kano.