Rundunar yan sandan jihar Kano, ta wa yi jami’anta shida Karin girma tare da lika mu su sabbin mukamai a wani taro da ya gudana a wajen shakatawar manyan jami’an yan sanda na Police Officer Mess dake unguwar Bompai.
Kwamishinan yan sandan jihar wanda ya samu wakilcin mukaddashin kwamishinan yan sandan ,DCP Ahmed Umar Chuso, ne ya garonci bikin karin girman a yau Laraba.
Mukaddashin kwamishinan yan sandan jihar Kanon, DCP Amhed Umar Chuso, yaja hankalin jami’an da suka samu Karin girman su kara jajircewa, domin aiki ne ya karu akansu, kuma su kasance masu gaskiya da rikon amana a koda yaushe don samun ci gaban rundunar.
Kakakin rundunar yan sandan kano SP Abdullahi haruna Kiyawa, ya ce wannan rana ce ta farin ciki da ba za su manta da it aba, domin yan uwa da abokin arziki sun bayyana farin cikinsu.
Jami’an yan sandan shida sun samu Karin girman ne daga matakin Chief Supretendent of Police ( CSP) zuwa Asisstant Commitioner of Police ( ACP) wato mataimakan kwamishinan yan sanda.
- Yan Sanda Sun Tabbatar Da Tsintar Gawar Tsohon Shugaban Hukumar Shige Da Fice A Hotel
- Yan Sandan Kano Sun Bankado Gungun Mutanen Da Suke Yaudarar Samari A Facebook Ciki Harda Yan Sandan Bogi.
SP Kiyawa ya kara da cewa tabbas rundunar ta samu gagarimin ci gaba kasancewar ma’aikatan ne suka samu Karin girman.
Haka zalika mukaddashin kwamishinan yan sandan ya ce su ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu tare da taimakawa al’umma.
Wadanda suka samu karin girman sun hada da , ACP Suleiman Jibrilla, ACP Husaini Yalwa Mohammed, ACP Isiyaku Mustapha Daura, ACP Mallam Garba Audu, ACP Jamilu Mohammed da kuma ACP Ibrahim Umar Makarfi
Suma wadanda suka samu Karin girman sun bayyana farin cikinsu tare da yin godiya ga Allah subahanahu wata’ala da ya nuna mu su wannan rana.
Taron Karin girman ya gudana ne a wajen shakatawa na manyan Jamian yan sandan jihar kano, dake unguwar bompai Kano , inda ya samu halattar manyan Jamian yan sanda da yan uwa da iyalan wadanda suka samu Karin girman.