Rundunar yan sandan Kano taja hankalin masu nemen aikin yan sanda su kula da yan damfara da sunan hukumar aikin yan sanda

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana cewar ta fara farautar wasu yan Damfara, dake yin lillibi da fatar Akuya, inda suke gabatar da kansu a matsayin Mambobin hukumar daukar ma’aikatan yan sanda ta kasa, don kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu, su fuskanci hukunci.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, a ci gaba da tantance wadanda suke da sha’awar shiga aikin jami’an tsaron yan sanda, wanda aka fara tantancewar, tun a ranar litinin din da ta gabata.


SP Abdullahi Haruna Kiyawa , yaja hankalin wadanda suka nemi shiga aikin yan sandan, su kara kula da yan damfara domin ba a biyan ko sisin kobo, kawai cancanta ake da bukata.

Da ta ke jawabi, Mukaddashiyar kwamishinan yan sanda dake jagorantar tawagar aikin tantancewar, DCP Zainab A. Pembi, ta yaba wa dukkan ma’aikatanta, bisa kwazon su da jajircewa , tare da yin kira a gare su , da su kaucewa duk wata hanya da ta saba wa doka kamar yadda idongari, ya ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, wanda kakakin rundunar yan sandan jahar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wakilta ya tunatar da tawagar ma’aikatan kan su yi aikin bisa umarnin babban sufeton yan sandan Nijeriya da kuma shugaban hukumar kula da aiyukan yan sanda, musamman wajen bin ka’idojin tantancewar yadda ya kamata.

TALLA

 

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya gargadi masu irin wannan mummunan hali da su chanja niya, domin duk wanda ya zo zai fuskanci hukunci.


Haka zalika rundunar ta bayar nambar wayar karta kwana ga duk wanda aka samu da aiyukan damfarar da shafi aikin tantacewa wadanda ake saran za a dauka aikin yan sandan Nijeriya, 08069794453 ko 09060483893.

Ya kuma godewa al’ummar jahar Kano, bisa goyon bayan da suke bayar wa a koda yaushe, harma ya yi kira a gare su a duk lokacin da suka wani da ba su amince da shi ba, su gaggawar sanar wa a ofishin yan sanda mafi kusa dan daukar matakin da ya dace ta wadannan hanyoyi :- 08032419754, 08123821575, 09029292926, ko NPF Rescue Me Application.

Facebook: Kano State Police Command
Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)
Instagram: Kano State Police Command
Tiktok: Kano State Police Command.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *