Rundunar yan sandan Kano tare da hadin gwiwar Equal Access International sun gudanar da wata tattauna wa da sauran hukumomin tsaro

Spread the love

Daga: Mujahid Wada Musa Kano

Rundunar yan sandan jahar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar Equal Access International, sun gabatar da taron tattauna wa, don ci gaba da wayar da kan al’umma hanyoyin da yakamata su bi wajen sanar wa da jami’an yan sanda bayanan sirrin da za su taimaka don dakile aikata miyagun laifuka.

Taron wanda aka gudanar da shi a shelkwatar rundunar yan sandan jahar Kano, karkashin jagorancin kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, da kuma sauran gamayyar hukumomin tsaron jahar.

Ma’aji Peters

Shugaban kungiyar Equal Access International, Ma’aji Peters, ya ce sun fara wani aiki ne a kananan hukumomin Gezawa, Ungoggo da kuma Nasarawa dake jahar, shi yasa suke tattauna wa da shugabannin hukumomin tsaro don sanar da su abubuwan dake faruwa a cikin al’umma.

Ma’aji Peters, ya kara da cewa, suna wayar da kan jama’a aduk lokacin da suka ga wani na ba daidai ba, su san wanda za su iya fada wa domin daukar matakin da ya dace da kuma yada za su iya yin magana da su.

ya kuma ce kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, yana bayar da goyon baya sosai harma da sauran hukumomin tsaron jahar kamar yadda Idongari.ng, ya ruwaito .

CP Muhammed Usaini Gumel

Anasa jawabin kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gueml, (Fada da cikawa) ya bayyana cewa irin wadannan kungiyoyi suna bayar da muhimmiyar gudunmawa, wajen inganta tsaro ta hanyar bayar da bayan sirri.

CP Gumel, ya ce suna kungiyar Equal Access International, suna da kwararrun mutane da suke shiga lungu da sako tare da tattauna wa da al’umma don su jiyo al’amuran da suke faruwa.

” Irin wannan tattauna wa da muke gudanar wa kamar wannan yana bamu damar karbar shawarwarin da za mu bi domin tuntubar al’umma wajen dakile matsalar tsaro a yankunnan karkara da kuma wuraren da akafi aikata su” CP M.U. Gumel.

Wata babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren karar da aka shigar da mawaki Rarara bisa zargin sukar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kano: Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa taron ya zama abun alkairi ga dukkan jami’an tsaro, tare da kira ga kungiyar su ci gaba da tattauna wa irin wannan.

Sai dai CP Muhammed Gumel, ya ce aikata laifuka yana sauya wa lokaci zuwa lokaci kasancewar kungiyar tana gudanar da aikin ta ne a kananan hukumomin, Gezawa, Nasarawa da kuma Ungoggo, inda ya ce yanzu kananan hukumomin da sukafi damun su , sune wadanda suke makota da jahohin Bauchi, Plato, Katsina da jahar Kaduna wadanda suke kewaye da jahar Kano.

ASP Abdullahi Hussaini (2ic)PPRO Kano.

” Idan ka lura a yanzu jahar Kano a kewaye ta ke da duk inda ake aikata laifukan ta’addanci, Garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, kuma Allah ya tsaro mana Kano babbu wani waje ayau da za ace yan ta’adda sun kwace ko sun rinke suna yin abunda suka dama kamar yadda yake faruwa a makotan mu” CP Gumel’‘.

M.U. Gumel, ya kara da cewa hukumomin tsaron dake aiki a jahar Kano kan su a hade yake, domin tattaunarwa su daya ce kafin su aiwatar da wani abu shi yasa suke samun nasarori akoda yaushe.

Ya bayar da misalin kan abubuwan da suka faru a kananan hukumomin Rogo, Karaye, Tsanyawa, Kunchi, Takai da kuma Sumaila, inda suka samar da jami’an tsaron hadin gwiwa bayan sun tuntubi gwamnatin jahar Kano, inda suke gudanar da sintiri a koda yaushe domin al’umma su yi bacci da idanun su.

” ko a kwanannan a yankin kwanar Dangora dake karamar hukumar Kiru da aka yi garkuwa da wani Kansila da kuma wani mai kudi har aka karbi kudin fansa sannan aka sake su, amma mu jami’an tsaro ba mu tsaya ba mun ci gaba da gudanar da bincike har muka samu nasarar kama mutane biyu da ake zargi da aikata laifin inda ake ci gaba da gudanar da bincike” CP Gumel”.

Taron ya samu halattar gamayyar hukumomin tsaro da suka hada da yan sanda, DSS, sojin kasa,sojin sama, sojin Ruwa, civil Defense, kwastam, NDLEA , dai dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *