Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama akalla batagari 15 da take zargi da aikata laifuffuka daban-daban a jihar.
Sanarwar da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar a jiya Juma’a ta ce, an kama gungun ‘yan fashin ne a ranar 8 ga watan Satumbar da muke ciki, da misalin karfe 2 na rana, lokacin da jami’an ‘yan sanda daga yankin Funtua suka kai samame a bisa samun bayanan sirri.
- Hukumar Shari’a Ta Kano JSC Ta Ladabtar Da Ma’aikatanta 2 Kan Badakalar Filaye.
- Gwamnatin Kano Za Ta Yi Duk Mai Yi Wuwa Don Samar Da A Asibiti A Unguwar Dangwauro: Abubakar Labaran
Ya kara da cewa an yi nasarar kwato banduran atamfofi 94 da leshi-leshi da bandura 2 na yadudduka, da aka kiyasta kudinsu zai kai naira miliyan 4 yayin samamen.
Har ila yau, rundunar ta cafke wasu mutane 3 da take zargi da mallakar bindiga kirar gida, a matsayin wani bangare na matakan da take dauka na karfafa aniyarta ta magance laifuffuka da tabbatar da zaman lafiyar al’umma.