Rundunar yan sandan Nigeria shiya ta , Kano da Jigawa ta bayyana shirin ta na zaben ranar Asabar.

Spread the love

Mataimakin sufeton yan sandan Nijeriya shiya ta daya dake jahar Kano, AIG Umar Mamman Sanda, ya bayyana cewa zaben da za a gudanar a ranar Asabar 3/2/2024, ya shafi Kananan hukumomin, Kunchi, Tsanyawa, Kura, Garin malam, Tofa, Rimin gado, Birnin Kudu da Kuma Buji dake jahohin Kano da Jigawa, inda suka shirya tsaf don tabbatar da tsaro.

Mai magana da yawun rundunar shiya ta daya CSP Bashir Muhammad , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a yau Juma’a,

CSP Bashir Muhammad, ya ce an takaita zirga-zirgar ababen hawa, a dukkanin wuraren da zabukan ya shafa.

Zabe: Muhimmiyar sanarwa daga rundunar yan sandan Kano

Yan Sanda Sun Kama Masu Buga Jabun Kudi 12 A Gombe

Sanarwar ta shawarci yan siyasa da magoya bayansu , su kiyaye da ka’idojin hukumar zabe , domin ba za a bar kowa ya yi abunda ya saba da doka ba.

Haka zalika rundunar shiya ta dayan, ta kara da cewa, za su yi aiki da sauraran hukumomin tsaro, don ganin an tabbatar da tsaro kafin zaben da ma bayansa, kamar yadda babban sufeton yan sandan Nijeriya , IGP Kayode Adeolu Abegtekun ya bada umarni.

A karshe rundunar ta yi fatan za a bada hadin kai domin gudanar da aiyukan zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *