Rundunar Yan Sandan Nigeria Ta Karrama Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano Da Nambar Yabon Da Yafi Kowanne Jami’in Hulda Da Jama’a Kwazon Aiki.

Spread the love

 

Rundunar Yan Sandangeria, ta karrama wasu hazikan jami’an ta, wadanda suka ciri Tuta wajen gudanar da aiyukansu.

Babban sufeton Yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Abegketun, ne ya jagoranci gudanar da Babban taron da aka Yi a Babban dakin taro na Hilton dake Babban birnin Tarayya Abuja a Ranar Litinin.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne Wanda yafi kowanne jami’an hulda da jama’a na jahohin Nigeria jajircewa kan aikinsa.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa SP Abdullahi Kiyawa, ya ciri tutar ce sakamakon yadda yake fitar da dukkan wani Abu da ya faru a jahar Kano, ta Hanyar amfani da kafafen yada labarai da kuma shafukan sada zumunta.

Kakakin Yan sandan jahar Kano, a lokuta daban-daban ya kan ja hankalin al’umma wajen bin doka da oda tare da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo razani ko fitar al’umma a sanarwar da ya fitar wa.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kawo gagarumin sauyi, ga rundunar Yan sandan Kano, wajen isar wa da al’umma sako cikin kankanin lokaci.

Jahar Kano, jaha ce da ta ke da gidajen radio fiye da 30 , gidajen Telebijin 10 da kuma Jaridun wadanda ake wallafa wa a yanar gizo-gizo, inda yake gabatar da shirye-shirye don wayar da kan al’umma akan abin da ya shafi tsaro da kuma gujewa aikata laifi.

Akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da yan jarida, wajen gudanar da mu’amulla ta yau da kullum , dare da rana yakan saurari duk Wanda yake neman karin Haske kan wani abu.

Tuni dai al’ummar jahar Kano, suka taya shi murna kan wannan nasara da ya samu tare da Yi masa fatan alkairi anan gaba.

Gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf Yusuf, na daga cikin manyan baki da suka halacci taron girmama hazikan yan sandan da nambar girmama wa , bisa jajircewa akan aiyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *